Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Masu Ruwa Da Tsaki Su Yi Sulhu Kan Takaddamar Zaben Najeriya - Nana Akufo Addo


Shugaban Ghana Nana Akufo
Shugaban Ghana Nana Akufo

Shugaba Akufo-Addo ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a zaben shugaban kasar Najeriya da aka kammala, da su yi sulhu cikin lumana ga dukkan wata takaddama da ta taso.

ACCRA, GHANA - Shugaban ya ce wannan ita ce hanya mafi dacewa wajen tunkarar kalubalen bayan zaben da mutanen kasar suka gudanar a ranar Asabar, 25 ga watar Fabrairu, 2023.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Shugaba Akufo-Addo ya fadi haka ne yayin da yake jawabi ga jakadun diflomasiyya a taron gaisuwar sabuwar shekara da aka saba yi duk shekara a Peduase Lodge dake yankin Gabas.

Ya ce, “ba zan iya kammalawa ba a yau, ba tare da nuna goyon bayan al'ummar Ghana ga babbar makwabciyarmu, tarayyar Najeriya ba, yayin da suke fuskantar kalubalen zaben sabbin shugabannin kasa. Ina fatan za a warware wannan rikicin cikin lumana bisa tsarin da ya dace”.

Shugaban ya kara da cewa, abubuwan da ke faruwa a Najeriya suna da tasiri kai tsaye ga sauran kasashen yammacin Afirka da ma nahiyar Afirka baki daya. Idan aka yi la’akari da haka, ya kamata masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa a Najeriya su lalubo hanyoyin samun bakin zaren cikin ruwan sanyi.

INEC ta ba Tinubu Shaidar lashe zabe
INEC ta ba Tinubu Shaidar lashe zabe

Bayan an kammala hada duk kuri’u na zaben shugaban hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta, INEC, Yakubu Mahmood ya bayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben, kuma zababben shugaban kasa, da safiyar Laraba a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.

Duk da cewa an samu tsaiko nan da can wajen gudanar da zaben, amma al’ummar Ghana sun bayyana fatan alheri ga kasar Najeriya da sabon shugaban da aka zaba.

Sun yi addu’a Allah Ya sa talakawan Najeriya su ce Alhamdulillah da wanda aka zaba, kuma suka yi kira da zaman lafiya bayan zaben, sannan kuma suka yi kira ga abokan takaran zababben shugaban da su yi hakuri, gaba da yawa.

A ranar 11 ga watan Maris 2023 ake sa ran gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun Jihohi a kasar ta Najeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Idris Abdullah:

Shugaba Akufo Addo Ya Yi Kira Ga Masu Ruwa Da Tsakin Najeriya Da Su Yi Sulhu Kan Takaddamar Zabe.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG