Hukumomin Nijar sun ayyana rana Talata a zaman ranar hutu a fadin kasar, bayan kwashe daren jiya na 27 na azumin watan Ramadan, domin dacewa da daren Lailatul Kadir, inda a ka kwana ana yi wa kasar da askarawan ta addu'o'in samun zaman lafiya.
Hukumar sadarwar jamhuriyar Nijar, ta kudiri aniyar samar da karin kudaden tallafi ga kafafe yada labarai masu zaman kansu kamar yadda abin yake a wasu kasashen yammacin Afrika ta yadda za su kara inganta ayyukan watsa labarai da tsara shirye-shiryen ci gaban kasa.
Kungiyar hadin kan kabilun Nijar wato NSC a takaice ta shirya bikin rarraba tufafin sallah da kayan abinci domin yara marayu da nufin ba su damar samun walwala kamar sauran yaran da iyayensu ke raye.
Wani sabani da ya shiga tsakanin Shugaban kasar Sudan na Soji Abdul Fattah Durham da shugaban dakarun 'yan tawayen RSF Muhammad Hamdan Dagalo bayan kin amincewar Durham da yarjejeniyyar zaman sulhun na shirin mika mulkin kasar ga farar hula domin dawo da kasar a tafarkin demokradiyya.
Kazamin fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da babbar rundunar mayakan kasar ta RSF a birnin Khartoum da wasu wurare a kasar, lamarin da ke kara kawo fargabar ganin bazuwar tashin hankali a kasar da ke fama da rikice-rikice.
Ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta tabbatar da labarin kama wasu ' yan kasar a Saudiya dake dauke da miyagun kwayoyi. Sai dai kawo yanzu ba a yanke musu hukunci ba kuma ba a san makomar su ba a cewar hukumomi.
Rundunar sojin Sudan ta yi gargadi a jiya Alhamis kan yiwuwar barkewar arangama da dakarun sa kai na kasar masu karfi, wadanda ta ce an girke su tura a Khartuom, babban birnin kasar da sauran wasu yankun ba tare da amincewar sojoji ba.
Shugabanin kungiyoyin manoman albasa da masu fitar da ita kasashen ketare sun koka a game da babbar asarar da matsalolin tsaro ke haddasa wa wannan fanni inda ‘yan ta’addan Burkina Faso ke kona motoci dauke da lodin albasa akan hanyarsu ta zuwa Cote d'Ivoire da Ghana
An bude wani taron masana na jahohi 8 na kasar don bitar ayyukan raya filayen noma da na kiwo a Nijar da zasu sa a samu wadataccen abinci a kasar da hana matasa tafiya cin rani.
‘Yan adawa a Majalisar dokokin Jamhuriyar Nijer sun bayyana damuwa dangane da yadda bangaren rinjaye ke haddasa cikas ga tsarin sulhun dake tsakanin bangarorin siyasar kasar.
Kasar Faransa ta gargadi ‘yan kasar ta su guji yawo a cikin kasashen Yankin Sahel da daina zuwa yawon bude ido a cikin wadanan kasashen don gudun sace su ko kuma a kashe su, biyo bayan karuwar aika-aikar ‘yan ta'adda a kan ‘yan kasar Faransa.
Domin Kari