Hukumomin Jamhuriyar Nijar da hadin guiwar kamfanin SONIMA sun kaddamar da ayyukan rajistar kananan bindigogin da ke hannun jama’a da nufin tantance fararen hular da suka mallaki makamai don takaita hadarin da ke tattare da rike bindiga ba akan ka’ida ba.
Rikici tsakanin Fulani da Tiv na jihohin Taraba da Benue a Najeriya ya ketare iyaka zuwa Kamaru inda mazauna iyakar suke fama da hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.
Yau Litinin ake shirin kammala bukukuwan Ista da Kiristocin duniya ke yi na tuna da daya daga cikin tushen imanin Kirista: mutuwar Yesu da kuma tashinsa daga matattu, bikin da aka dauka babban al’amari a Ghana, inda Kiristoci ke shirya yadda za su gudanar da wadannan ranakun Ista masu muhimmanci.
Sabon Shugaban Musulmi a majalisar dokokin kasar Ghana kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar Yendi da ke arewacin Ghana, ya ce suna kokarin ganin an gaggauta amincewa da dokar auren Musulmi da saki a kasar.
Dakarun tsaro a Kamaru na neman akalla mutane 25 da 'yan bindiga suka sace a kan iyakar kasar da Najeriya. Al’ummar yankin na kira ga gwamnatoci da su dauki matakan dakatar da kungiyoyin ‘yan bindiga da ke aiki a bangarorin iyakar biyu, a cewar rahoton Moki Edwin Kindzeka wakilin Muryar Amurka.
Gwamnatin Nijar ta bayyana damuwa a kan yadda matsalar 'yan bindiga ta ki karewa a cikin kasar da kuma yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.
Kungiyar tarayyar turai ta ayyana shirin bada tallafin makamai wa wasu kasashen Afrika masu fama da matsalolin ta’addanci wadanda suka hada da Jamhuriyar Nijer da Somalia
Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa Reporters Sans Frontieres wato RSF a takaice ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira yanayin tsaka mai wuyar da ‘yan jarida suka shiga a yankin Sahel.
Yara da mata suna cikin rukunin al'ummar da ya fi jin radadin matsalolin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a wannan yankin na Afirka musamman mata wadanda suke cikin barazanar lalata.
Daga Sapeliga a gundumar Bawku ta yamma a jihar maso gabashin kasar Ghana, daruruwan ‘yan gudun hijira daga Burkina Faso na ci gaba da neman mafaka a Ghana.
Domin Kari