Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Nijar Sun Yi Hutun Daren Laylatul Qadr


Hukumomin Nijar sun ayyana rana Talata a zaman ranar hutu a fadin kasar, bayan kwashe daren jiya na 27 na azumin watan Ramadan, domin dacewa da daren Lailatul Kadir, inda a ka kwana ana yi wa kasar da askarawan ta addu'o'in samun zaman lafiya.

BIRNIN N’KONNI, NIGER - Tun daga shugaban kasar Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazum a massalacin fadar sa, izuwa Firai ministan Jamhuriyar Nijar Uhumudu Mahamadu da membobin majalisar ministocinsa da shugaban majalisar dokoki ta kasa Seini Umaru da ‘yan majalisar dokokin na wannan kasar da malaman addinin Islama da ‘yan kasar Nijar maza da mata na birane da kauyuka duk sun kwashe tsawon daren jiya na 27 ga watan azumin Ramadan, da ake hasashen dacewa da daren Lailatul Kadari.

An roki ko wane ‘dan kasa da ya daga hannu sama ya roki Allah, domin samun zaman lafiya a cikin kasar da ‘yan ta'adda suka zagaye, da kuma samun galaba ga askarawan kasar.

Wannan ne ya sa gwamnatin kasar ta baiwa ma'aikata hutu a yau Talata domin hutawa tare da ramakon baccin daren da suka share a jiya sunawa kasar addu'o'i.

Malam Mudaha wani malamin addinin islama ya ce hakan yayi dai-dai yadda gwamnati kasar ta yi.

Suma ma'aikatan kasar da ke morewa wannan ranar ta hutu ta yau Talata sun nuna gamsuwarsu game da abinda gwamnatin tayi musu da ma addininsu, tare da rokon Allah da aka yiwa kasar a cikin daren na jiya inji malam Salifu Mahamadu Wety wani ma'aikacin gwamnati.

Shima wani malam Yahaya ya nuna godiya a madadin sauran ma'aikata ‘yan uwansa domin kebe wannan ranar da gwamnati yayi don hutawa bayan kwana addu'o'in neman kasar ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Su dai ‘yan Nijar, suna ganin abu daya da zai taimakawa kasar tun daga sojojin ta izuwa hukumomi da ma sauran al'ummar ta wajan samun tsaro da zaman lafiya, shine addu'o'in da al'ummomin kasar keyi ba dare ba rana domin samun zaman lafiya.

Saurari cikakken rahoto daga Harouna Mamman Bako:

‘Yan Nijar Sun Yi Hutun Aiki Yau Bayan Kwana Yin Addu’o’i Daren Laylatul Qadr.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:39 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG