An gudanar da taron ne karkashin hukumar tallafa wa kasashe masu tasowa ta Amurka da takwarar ta Nijar,
Ma'aikatun ministocin gidan gona, da na filaye da na kiwo, da kuma gandun daji sun tattaro masana kan harkar filaye na jihohi 8 dake Jamhuriyar Nijar a karkashin hukumar tallafa wa kasashe masu tasowa ta Amurka (MCC Millenium Challenge Cooporation) da takwararta Jamhuriyar Nijar MCA-Niger (Millenium Challenge Account Niger), game da filayen da hukumar MCC ta Amurka ta bada tallafin sama da biliyan 300 na CFA domin rayasu da nufin bunkasa noma da kiwo a jihohin kasar, don samar wa kasar wadataccen abinci da kuma hana matasa zuwa kasashen waje ci-rani.
Maitre Sa'adu Aladuwa, shi ne masanin dokokin kasar a wurin taron da ake yi a garin Birni N'Konni, ya ce an sun je taron ne don duba ayyukan da aka yi da kudin tallafin da suka shafi gandari don kawo ci gaba wajen bunkasa harkar noma da kiwo.
A cewar malam Ibrahim Suley, masanin harkokin noma na ma'aikatar Ministan gidan gona a Nijar, taron zai jawo hankalin ‘yan kwangilar da aka baiwa aikin raya filayen noma da na kiwo da su hada hankalinsu wuri daya, maimakon akasin haka.
An dai yi tanadi a wannan aikin na raya filayen noma da kiwo a Nijar da tallafin kasar Amurka ne don baiwa mata, da matasa, da nakasassu wani kaso don su samu abin dogaro da kai, amma a wurin taron mata sun ce sai gafara sa suke ji ba a ganin kaho.
Wannan taron da ke wakana a garin Birni N'Konni ya samu halartar mahakunta na Bariki da na gargajiya kuma tsawon kwanaki 3 za shafe ana yinsa.
Saurari rahoton Harouna Mamane Bako: