Wasu al'ummar Jamhuriyar Nijar mazauna Ghana sun bayyana ra'ayoyi mabambanta game da hambarar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar, inda wasu ke cewa hakan ya yi daidai, wasu kuma suna ganin matakin wani koma baya ne ga dimokradiyyar kasar.
Rundunar sojan Nijar da ta kwace mulki a makon da ya gabata tare da hambarar da zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, ta zargi gwamnatin hambararren shugaban kasar da bai wa Faransa izinin kai hari akan fadar shugaban kasar domin kokarin kubutar da Bazoum.
Shugaban kasar Chadi ya isa birnin Yamai a yammacin ranar Lahadi jim kadan bayan kammala taron kungiyar kasashen ECOWAS.
Jama'a na ci gaba da bayyana ra'ayoyi mabambanta game da matakin da kungiyar ECOWAS ta dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da umarnin su maida mulki hannun farar hula.
Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS ta dauki matakin kakabawa jamhuriyar Nijar takunkumi tare da baiwa jagoran mulkin wa’adin kwanaki bakwai ya mika mulki ga gwamnatin farar hula.
Shugabanin kasashen kungiyar ECOWAS za su gudanar da taro a Abuja don tantauna inda zasu bullo wa sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar.
Ana ci gaba da samun ra'ayoyi mabambanta game da juyen mulki da wasu sojoji a karkashin jagorancin Janar Abdurahamane Tchiani suka gudanar a cikin wannan makon a Jamhuriyar Nijar.
Jam’yar PNDS Tarayya madugar kawancen jam’iyun hambarariyar gwamnatin Nijar ta musanta zargin hannun tsohon Shugaban kasa Issouhou Mahamadou, a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar Larabar ta gabata.
Tsohon Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi mamakin jin cewa an yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum Mohammed.
Sojojin da suka kifar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar Larabar da ta gabata a Jamhuriyar Nijar sun zabi kwamandan rundunar tsaron fadar Shugaban kasa General Abdourahamane Tchiani a matsayin shugaban majalissar CNSP domin ya jagoranci al’amuran kasar.
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan ta’adda ne da ke da alaka da kungiyar IS, sun kashe mutane 32 da suka hada da makiyaya 25 a wasu hare-hare guda biyu da aka kai a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mataimakiyar Shugaban kasar Amurka Kamala Harris ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Nijar ta kuma bayyana damuwa matuka kan lamarin a wata ganawa da ta yi da shugaban Najeriya Bola Tinubu ta wayar tarho, a cewar wata sanarwa da fadar White House ta fitar.
Domin Kari