Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Na yi Mamakin Juyin Mulkin Da Sojoji Suka Yi A Nijar: Buhari


Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)
Shugaba Buhari (Instagram/ muhammadubuhari)

Tsohon Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi mamakin jin cewa an yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar, wanda ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum Mohammed.

Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na twitter inda ya bayyana farin ciki da matakin da wanda ya gaje shi Bola Tinubu ya dauka, ya kuma ce yana da kwarin gwiwar cewa shugaban Najeriya zai iya shawo kan matsalar..

Buhari ya ci gaba da cewa, “kamar yadda ake sa zuciya, Ni ma, kamar sauran miliyoyin ‘yan Najeriya, na yi matukar kaduwa da abubuwan da su ka faru a baya-bayan nan a Jamhuriyar Nijar”

Janar Abdouramane Tchiani
Janar Abdouramane Tchiani

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma bayyana damuwa dangane da makomar tsarin damokaradiyya a yankin baki daya da kuma makomar Shugaba Mohammed Bazoum da iyalinsa.

Yace kamar sauran mutane, shi da maidakinsa, sun damu matuka, sai dai ya bayyana jin dadin ganin yadda kungiyar ECOWAS, karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta dauki matakin samar da masalaha, tare da fatar za’a sauya lamarin a kuma kare lafiyar Shugaba Bazoum da iyalinsa.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG