Masu sharhi kan lamuran siyasa da diflomasiyya na ganin cewa yunkurin juyin mulkin da aka yi a Nijar sam bai zo da mamaki ba, idan aka yi la'akari da tarihin rikicin siyasar kasar da ke yammacin Afirka.
Wasu masu zanga-zangar goyon bayan sojojin da suka yi juyin mulki a kasar sun yi kaca-kaca da ofishin jam’iyar PNDS mai mulki a yau Alhamis tare da kwasar ganima da farfarsa gilasai da kona gomman motoci.
Bangarorin siyasa a Jamhuriyar Nijar sun fara maida martani bayan da wasu sojoji suka ba da sanarwar kifar da shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki a ranar Laraba 26 ga watan Yuli, yayin da jam’iyar PNDS mai mulki ke cewa za ta yi gwagwarmaya don mayar da hambararen shugaban akan kujerarsa.
A ranar Alhamis ne rundunar sojojin Nijar ta bayyana goyon bayanta ga juyin mulkin da sojoji masu tsaron fadar shugaban kasar suka yi, inda rundunar ta ce abin da ta sa a gaba shi ne kaucewa ta da zaune-tsaye a kasar.
Ta tabbata sojoji sun yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijer a jiya laraba.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Talon ya kai wa Tinubu a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.
Majalisar Dokokin Ghana ta kada kuri'ar soke hukuncin kisa, wanda ya sa kasar ta kasance ta baya-bayan nan cikin jerin kasashen Afirka da dama da suka yi yunkurin soke hukuncin kisa a shekarun baya-bayan nan.
Cikin wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta yi kira ga dakarun da ke da hannu a yunkurin juyin mulki da su hanzarta sakin shugaban kasar saboda an zabe shi ne bisa tsarin mulkin dimokradiyya.
“Bayanai na nuni da cewa Shugaba Mohamed Bazoum na hannun dogarawan fadarsa." In ji wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta kafa wannan dokar ne ta hana fitar da hatsi da shinkafa daga kasar a matsayin wani mataki na kare karancin abinci a kasuwannin kasar.
Ministan cikin gidan Jamhuriyar Nijar ya ziyarci wasu gundumomin jihar Tilabery da nufin kwantar da hankulan mutanen da suka tsere daga matsugunansu bayan da a farkon watan nan na Yuli ‘yan ta’adda suka umurce su da su fice daga garuruwan ko kuma su kuka da kansu da abin da zai biyo baya.
Domin Kari