Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Juyin Mulki Ba Zai Magance Matsalar Tsaro A Nijar Ba - Masana


Taron ECOWAS
Taron ECOWAS

Wasu al'ummar Jamhuriyar Nijar mazauna Ghana sun bayyana ra'ayoyi mabambanta game da hambarar da gwamnatin farar hula a Jamhuriyar Nijar, inda wasu ke cewa hakan ya yi daidai, wasu kuma suna ganin matakin wani koma baya ne ga dimokradiyyar kasar.

Rabiu Abarshi, dan asalin jihar Tahoa, ya bayyana cewa suna farin ciki da juyin mulki da aka yi saboda matsalar tsaro da wani abin da ya kira muzgunawa wadanda ba su goyon bayan jamiyyar PNDS tarayya.

"Ni gaskiya juyin mulki da aka yi y ayi min dadi saboda babu tsaron kasa kuma ana kashe sojoji. Ko a kauyenmu barayi sun yi mana yawa, sannan kuma in kai ba dan jamiyyar PNDS tarayya ba ne ko ka na da gaskiya, ba za'a ba ka gaskiya ba"

Shi kuwa Abdullahi Adamu dan jihar Maradi mazauni Kumasi na kasar Ghana mai goyon bayan jamiyyan PNDS tarayya, ya bayyana damuwarsa matuka akan wannan juyin mulki da aka yi tare da musunta zarge-zargen da ake yi wa jamiyyarsa ta PNDS tarayya inda yake cewa;

"Ikirarin duk na adawa ne kuma wannan juyin mulki da aka yi bai yi mana dadi ba, an maida mana abubuwa baya, komai an durkushe mana. Abin da na ke so in da hali, a maida gwamnatin farar hula kan mulki"

Shima Abdullai Poja dan Nijar, damuwarsa shine matsalar tsaro da suke fama da ita a duk lokacin da za su koma gida, abin da yake neman a magance musu.

"Duk lokacin da za mu koma gida Nijar muna cikin fargaba saboda matsalar tsaro, amma in dai sojojin da suka kifar da gwamnati za su iya su samar da tsaro, ta yadda za mu iya shiga mu fita Nijar, zamu yi farin ciki"

Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin Abubakar Illolu, daya daga cikin shugabannin PNDS tarayyar a kasashen waje kan ikirarin muzgunawa wadanda ba su da alaka da jam’iyyar, amma yunkurin ya ci tura.

Matsalar tsaro na kan gaba cikin dalilan da dakarun soja suka bayar na daukar matakin hambararda gwamnatin Bazoum Muhammad, amma Umar Sanda Ahmad, mai sharhi kan sha'anin tsaron ciki da wajen Ghana, na ganin matsalar tsaron kasar za ta iya ta'azzara sakamakon wannan juyin mulki.

"Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kasashe matalauta a duniya kuma abin da ya sanya wasu kasashe kamar Rasha suke neman karfafa alaka da su shine ma'adanin Uranium da suke da shi don saboda Rasha tana bukata. Za'a iya cewa wasu kasashen waje na da hannu a cikin juyin mulki da aka yi saboda an ga wasu al'ummar kasar Nijar dauke da tutocin Rasha, abin da ke nuni da cewa basu ji dadin kawancen Nijar da Faransa ba. Idan aka ce matakin kifar da gwamnatin Bazoum zai karfafa tsaron kasar, zan iya cewa yayi wuyar gaske," inji shi.

Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tattalin arzikin Afirka ta yamma ECOWAS sun bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar wa'adin kwana bakwai su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum kan mulki ko kuma su dau matakin ba sani ba sabo a kan su.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Anthony Blinken, tare da hadin gwiwa da Kungiyar Ƙasashen Afirka da ECOWAS da Tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya, duk sun yi Allah wadai da juyin mulkin.

Saurari rahoton Hamza Adams a sauti:

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG