An kama wani mutum ranar Talata, kuma zai fuskanci tuhume-tuhume 76 na kisan kai bayan ya bada shaida a bincike cewa shi ya tayar da mummunar gobara a Afirka ta Kudu a bara a lokacin da yake kokarin kawar da gawar wani da ya shake, ya kashe a harabar gidan bisa umarnin wani dillalin miyagun kwayoyi
Wata motar dakon kaya da ke tsananin gudu ta kutsa cikin wani rafi a kudu maso yammacin Kongo, inda ta kashe fasinjoji 18 da ke cikinta tare da jikkata wasu fiye da goma, in ji 'yan sanda
Kasar Kamaru za ta kasance kasa ta farko da za ta rika bai wa yara sabbin rigakafin zazzabin cizon sauro a kai a kai, yayin da ake ci gaba da rarraba allurar ta rigakafi a nahiyar Afirka.
Dan shekaru 79 da haihuwa ya doke tsohon dan wasan kwallo, wadda ya taba lashe kyautar Ballon d'Or, George Weah a zagaye na biyu na zaben watan Nuwamba da kashi 50.64 na kuri'un da aka kada.
Shugaban Masar ya ce a ranar Lahadi kasarsa ta tsaya kafada-da-kafada da Somaliya a takaddamar da ke tsakaninta da kasar Habasha na tsakiyar ruwa, wadda ta kulla yarjejeniya da Somaliland domin samun damar shiga teku da kuma kafa sansanin sojojin ruwa.
A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwar Amurka da Afirka tun bayan taron Shugabannin Amurka da Afirka, da suka hada da yanayi, abinci, da kiwon lafiya.
Kasar Zambia na fama da barkewar cutar kwalara da ta kashe mutane sama da 400 kuma wasu fiye da10,000 sun kamu da cutar, lamarin da ya sa hukumomi suka ba da umarnin rufe makarantu a fadin kasar bayan hutun karshen shekara.
Firai Ministan gwamnatin rikon kwaryar Nijar, Lamine Zeine, ya isa birnin Mosco a kasar Rasha da nufin tattauna batutuwa da dama a wannan lokaci da Nijar ke fuskantar tarnaki daga kasashen yammacin duniya sakamakon kifar da gwamnatin dimokradiya.
Matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afirka ta fara aiki a Najeriya, kamar yadda kamfanin ya bayyana, wanda ya kawo karshen tsawon shekaru da aka kwashe ana jiran soma aikin masana'antar.
Isowar su tashar binciken ke da wuya suka shiga bude wuta.
Faduwar darajar Naira a Najeriya ya fara shafar wasu harkokin kasuwanci a makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar inda ma su harkokin kasuwanci ke cewa lamarin ya shafe su matuka.
Kotun hukunta laifukan soja ta Yamai ta sallami Salim Bazoum, dan hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum, a zamanta na jiya Litinin 8 ga watan Janairu bayan shafe sama da watanni 5 a tsare a fadar shugaban kasa, wuri guda da mahaifiyarsa Hadiza Bazoum da mahaifinsa Mohamed Bazoum ke tsare.
Domin Kari