Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masar Ta Ce Za Ta Tsaya Kafada-Da-Kafada Da Somaliya A Tsakanin Rikicinta Da Habasha


Abdel Fattah El-Sisi Shugaban kasar Masar (Egypt)
Abdel Fattah El-Sisi Shugaban kasar Masar (Egypt)

Shugaban Masar ya ce a ranar Lahadi kasarsa ta tsaya kafada-da-kafada da Somaliya a takaddamar da ke tsakaninta da kasar Habasha na tsakiyar ruwa, wadda ta kulla yarjejeniya da Somaliland domin samun damar shiga teku da kuma kafa sansanin sojojin ruwa.

WASHINGTON, D. C. - Shugaba Abdel Fattah El-Sissi ya yi fatali da yarjejeniyar da Habasha ta kulla da yankin da ke ballewa. Ya yi kira ga Habasha da ta nemi fa'ida daga tashar jiragen ruwa a Somaliya da Djibouti "ta hanyar wucin gadi," maimakon ta yunƙurin "mallake wani yanki ko kasa".

Shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud
Shugaban kasar Somalia Hassan Sheikh Mohamud

"Ba za mu yarda kowa ya yi wa Somalia barazana ko kuma a keta kasarta ba," in ji El-Sissi a wani taron manema labarai na hadin gwiwa a birnin Alkahira tare da shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud. “Kada wani ya yi kokari yi wa ’yan’uwan mu na Masar barazana, musamman idan ’yan’uwanmu sun ce mu tsaya tare da su.”

Somaliland, yanki ne da ke kusa da gabar tekun Aden, wanda ya balle daga Somalia a shekarar 1991, a daidai lokacin da kasar ta fada cikin rikici karkashin jagorancin shugaban yakin. Yankin dai ya ci gaba da rike gwamnatinsa duk da rashin amincewar da kasashen duniya suka yi masa.

Muse Bihi Abdi
Muse Bihi Abdi

Shugaban Somaliland Muse Bihi Abdi ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed a farkon wannan watan domin baiwa Habasha damar hayar wani yanki mai nisan kilomita 20 (kilomita 12.4) na gabar teku domin kafa sansanin sojojin ruwa.

Sheikh Mohamud, shugaban Somaliya, ya yi watsi da yarjejeniyar da cewa ya saba wa dokokin kasa da kasa, yana mai cewa: "Ba za mu nade hannu ba, muna kallo yadda ake cin zarafin 'yancinmu."

Ahmed Aboul Gheit
Ahmed Aboul Gheit

A karshen makon nan ne ya isa Masar domin nuna goyon baya ga gwamnatinsa. Ya gana da shugaban kungiyar kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit da babban Limamin masallacin Azhar, Sheikh Ahmed al-Tayeb.

Masar dai na da sabani tsakanin ta da kasar Habasha, game da takaddamar dam da kasar Habasha ta gina a babban mashigar kogin Nilu. Kasashen biyu tare da Sudan sun kwashe sama da shekaru goma suna kokarin cimma matsaya kan daidaito da gudanar da ayyuka na dala biliyan 4 na Grand Renaissance Dam.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG