Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 18 Suka Mutu A Hadarin Mota Da Ya Jefasu Cikin Kududdufi A Kongo


Wata motar dakon kaya da ke tsananin gudu ta kutsa cikin wani rafi a kudu maso yammacin Kongo, inda ta kashe fasinjoji 18 da ke cikinta tare da jikkata wasu fiye da goma, in ji 'yan sanda

WASHINGTON, D. C. - An makare motar da kaya kuma da kuma fasinjoji da yawa, a kan wata babbar hanya a yankin da ke nesa da yankin Kasangulu a gundumar Kongo ta tsakiya a ranar Lahadin da ta gabata lokacin da ta fada cikin kududdufi, a cewar kwamandan ‘yan sanda na Kasangulu Benjamin Banza.

“An kai gawarwakin da aka dauko daga rafin zuwa dakin ajiye gawa na babbar asibitin Kasangulu, yayin da wadanda suka jikkata su 6, da suka hada da manya da kananan raunuka, duk ana ba su jinya a asibitin,” in ji Banza da yammacin Lahadi.

Banza ya ce motar ta yi mummunan lalacewa kuma har yanzu ba'a iya ciro ta daga cikin kududdufin ba, ya kara da cewa ana zargin gudu ne ya haddasa hatsarin.

Tsananin gudu na daga cikin abubuwan da ke haddasa hadura a kan manyan tituna a kasar Kongo, inda galibi ba'a bin ka'idojin tuki.

Hatsarin na ranar Lahadi ya haifar da damuwa game da kiyaye hanyoyin mota a yankin Kongo ta Tsakiya, wanda a kai a kai ake samun irin wadannan rahotonin ibtila'in. Hukumomin yankin sun mai da martani tare da yin alkawarin ilmantar da direbobi da kuma tilasta bin doka da oda.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG