Shugaba Macky Sall, wanda ke kammala wa’adin mulkinsa na 2, ya dage lokacin gudanar da zaben Shugaban Kasar Senegal da watanni 10, inda ya kafa hujja da rashin kammala warware wasu rigingimu akan waye ya kamata ya tsaya takara.
A watan Janairu kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar suka sanar da shirinsu na ficewa daga kungiyar ta ECOWAS.
Hukumomin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar sun kori wasu kananan jakadun da ke wakiltar kasar a kasashe da dama na nahiyar Turai da Asia har ma da na kasashen Afrika.
Tsohon Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou ta bakin lauyansa ya musanta zargin da tsohon jakadan Faransa a Nijar ya yi cewa ya na da hannu dumu dumu a juyin mulkin da soja suka yi wa Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ce masu zanga-zangar suna zargin kasashen ne da goyon bayan Rwanda ta wajen amfani da 'yan tawayen M23.
Kungiyar alkalan shari’a wato SAMAN a Jamhuriyar Nijar ta maida martani bayan da Shugaban hukumar yaki da cin hanci ta COLDDEF ya ayyana shirin karbar wasu takardun binciken almundahana daga hannun mashara’antar kasar.
A jamhuriyar Nijar, an shiga kace nace a tsakanin sabuwar hukumar yaki da almundahana wato COLDDEF da tsohuwar hukumar HALCIA, bayan da shugaban hukumar ya zargi tsohuwar hukumar da lalata wasu bayanan binciken lamarin da ya ce ya na tarnaki ga aiyukan binciken da ke gudana a halin yanzu.
A Nijar, kungiyar lauyoyi ta zargi hukumar yaki da mahandama ta COLDDEF da tauye wa wasu kusoshin hambararriyar gwamnati da ta ke gudanar da bincike akansu damar cin moriyar ‘yancin samun kariya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Da alamar takaddamar Habasha da Somaliya na kara muni, ganin yadda har ta fara shafar huldarsu a AU.
Shugabannin kasashen Afirka sun bude wani taro na kwanaki biyu a ranar Asabar, yayin da nahiyar ke kokawa da juyin mulki da rigingimu da rikicin siyasa da kuma zaman dar dar a yankin.
Nahiyar Afirka har yanzu na ci gaba da Fuskantar barazana daga Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin addini ta IS yayin da ake fama da tashe-tashen hankula na siyasa a yammacin Afirka da yankin Sahel.
Masar na shirin shirya wani yanki a kan iyakar Gaza wanda zai iya daukar Falasdinawa idan har hare-haren Isra'ila a kan Rafah ya yi sanadin 'yan gudun hijirar zuwa kan iyaka, in ji majiyoyi hudu, a wani mataki da suka bayyana a matsayin wani yunkuri na gaggawa da birnin Alkahira ke shiryawa.
Domin Kari