Gangamin wanda ya sami halartar shugabanin majalissar soja ta CNSP shine na farko da aka shirya domin nuna kin jinin dakarun Amurka dake da sansani a yankin Agadez.
Gwamnatin rikon kwaryar jamhuriyar Nijar ta sanar da isowar wasu makamai da na’urorin kare sararin samaniyar da tace sun shigo ne albarkacin huldar ayyukan sojan dake tsakanin Nijar din da Russia.
A wata sanarwa da Rundunar sojin Nijar ta fitar, ta bayyana mutuwar sojoji 6 sakamakon wani harin bam a kusa da kan iyakar Nijar da Mali a ranar Alhamis.
Kimanin mutum miliyan 3 da dubu 400 ne ke bukatar agajin gaggawa a kasar Chadi sakamakon isowar dumbin ‘yan gudun hijirar Sudan da ke gudun hijira.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP, ya ce fursunoni 38 ne suka tsere daga wani gidan yari mai cunkoso a Moroni, babban birnin kasar, bayan da wani soja da aka tsare ya fasa gidan yarin.
Gwamnatin mulkin sojan Mali ta kafa wata doka da ta dakatar da ayyukan jam'iyyun siyasa, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Abdoulaye Maiga ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar da yammacin jiya Laraba.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dan tsere Russ Cook ya isa yankin arewacin Afirka, kusan shekara guda bayan ya tashi daga kudancin nahiyar a yunkurinsa na kure tsawon nahiyar da gudu.
Hukumar kula da shige da fice ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa, akalla bakin haure 38 da suka hada da kananan yara ne suka mutu a wani jirgin ruwa a gabar tekun Djibouti.
Cibiyar samar da zaman lafiya ta Amurka ta bayyana cewa. dole ne Amurka ta inganta huldar kasuwanci da kasashen Afirka domin dakile dogaro ga kasar China wajen samun ma'adanai masu mahimmanci.
Masana da kungiyoyin kasa da kasa da makiyayan sun soki abinda su ka kira son kai da kasashe masu galihu ke nunawa da ke zaman musabbabin sauyin yanayi da kasashen suka tsinci kan su a ciki
Wani jirgin ruwan katako na tsalake kogi ya nutse a gabar tekun arewacin Mozambique inda ya kashe mutane 94, ciki har da yara, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a yau Litinin.
Dakarun sojin Sudan sun kashe akalla mutane 28 a wani hari da suka kai a wani kauye da ke kudu da babban birnin kasar Khartoum, kamar yadda kwamitin likitocin kasar ya sanar a jiya Lahadi.
Domin Kari