Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ruwa Da Tsaki A Yankin Sahel Sun Kammala Taron Koli Kan Sauyin Yanayi


Taron makiyaya a Nijar na kasashen Sahel
Taron makiyaya a Nijar na kasashen Sahel

Masana da kungiyoyin kasa da kasa da makiyayan sun soki abinda su ka kira son kai da kasashe masu galihu ke nunawa da ke zaman musabbabin sauyin yanayi da kasashen suka tsinci kan su a ciki

AGADEZ, NIGER - A tsawon kwanaki uku masanan da kungiyoyin kasa da kasa da makiyayan sun soki irin son kan da suka ce kasashe masu galihu su ke nunawa a fannin sauyin yanayi, dake zaman musabbabin sauyin yanayi da kasashen suka tsinci kan su a ciki.

Masansan sun bayyana haka ne a wajen wani taro inda suka koka da irin halayen da kasashen ke nunawa wajen daukar matakin da zai rage illolin da sauyin yanayi ke haifarwa a kasashe marasa galihu irin na Sahel.

Taron na karon farko ya mayar da hankali ne kan hanyoyin da za’a bi don kaucewa irin illoli da asarar da sauyin yanayi ke haifar wa a yankin.

Mahalarta taron dai sun bukaci kudin diyya saboda irin asarar da suka tabka da ke haifar da wahalar bala’o’i da ake fuskanta a kasar kama daga ambaliyar ruwa, kwararowar hamada.

Makiyaya da suka halarci taron na ganin akwai bukatar a samar da shawarwari na bai daya wanda za a gabatarwa shugabannin yankin.

A karshe dai mahalarta taron sun fitar da wani dafatari domin jaddada mahinmancin yankin wajen zama mahinmin bangare inda ya kamata a karkata domin samun mafita kan sauyin yanayi dake addabar duniya.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:

Masana, Makiyaya Da Masu Ruwa Da Tsakin Yankin Sahel Sun Kammala Taron Kolin Kan Sauyin Yanayi.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG