Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Bam Ya Kashe Sojojin Nijar Shida


Jana’izar Wasu sojoji
Jana’izar Wasu sojoji

A wata sanarwa da Rundunar sojin Nijar ta fitar, ta bayyana mutuwar sojoji 6 sakamakon wani harin bam a kusa da kan iyakar Nijar da Mali a ranar Alhamis.

Majiyar ta bayyana cewa sojojin sun dawo daga aikin sintiri daga Inates ne bayan sun tsallake rijiya da baya inda suka taka wata nakiya da ke kusa da kauyen Tingara da ke kudu maso yammacin kasar.

Rundunar ta kara da cewa wasu sojoji sun jikkata kuma an kwashe su da jirgi mai saukar ungulu zuwa asibitin birnin Yamai.

Rundunar ta ce daga baya ta kai wani hari ta sama bayan da ta bi diddigin wadanda ta ce suna da hannu tare da ‘yantar da wasu da dama daga cikin wannan aiki na ta’addanci.

"An bi su zuwa wani yanki inda suka hada da kusan wasu masu hannu da shuni guda ashirin sannan kuma an kai harin ta sama, wanda ya ba su damar kashe wasu ‘yan ta’addan tare da lalata tarin makamai.”

A cikin wannan tsari, an sake kai wani hari ta sama a kan gungun 'yan ta'addan a yankin Amalaoulaou na kasar Mali, lamarin da ya baiwa rundunar tsaron ta Nijar damar kashe ‘ yan ta’adda takwas.

A watan da ya gabata, sojojin Nijar 23 ne suka mutu a wani harin kwantan bauna da ‘yan ta’adda suka kai a Tillaberi mai iyaka da Burkina Faso da Mali, kuma dukkansu a karkashin mulkin soja.

Har ila yau gwamnatin Yamai na fuskantar tashe-tashen hankula daga mayakan jihadi na Boko Haram da kuma 'yan ta'addar daular Musulunci ta yammacin Afirka (ISWAP) daga yankin kudu maso gabashin Diffa da ke kusa da Najeriya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG