Hukumomin rikon kwarya na Guinea sun gabatar da daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai rage tare da kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa, da kuma yiwuwar ba wa shugaban mulkin sojan kasar Mamady Doumbouya damar shiga zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wata kotu a jamhuriyar Nijar ta bada belin wasu daga cikin ministocin gwamnatin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum bayan shafe shekara guda a tsare a gidajen yari daban-daban na jihohin Tilabery da Dosso sakamakon zargin cin amanar kasa.
Wani mai shigar da kara a Congo ya bukaci wata babbar kotu a Kinshasa ta yanke hukuncin kisa a kan wasu mutane 25 da ake tuhuma da zama membobin kungiyar ‘yan tawayen M23
Sojojin hayan kungiyar Wagner ta kasar Rasha ta fada a ranar Litinin cewa mayakanta da sojojin Mali sun yi asara a wani kazamin fada da 'yan tawayen Abzinawa suka yi a kusa da kan iyakar Mali da Aljeriya.
Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 1.3 ne suka kamu da cutar HIV mai karya garkuwar jiki a shekarar 2023, inda da yawa daga cikin wadanda suke fama da cutar ke a nahiyar Afirka, a cewar hukumar UNAIDS.
Iyalai da ke cikin juyayi sun cika gidaje a wani kauye da ke kudancin kasar Habasha a jiya Juma'a don yi wa ‘yan uwansu da suka mutu sakamakon mummunar zaftarewar laka da ta auku bankwana, yayin da hukumomi suka sanar da ayyana zaman makoki na kwanaki uku a kasar.
An ci gaba da kokarin ceto mutane har ya zuwa yammacin jiya Talata a yankin Gofa, bayan zaftarewar kasa yayi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 229 a kudancin kasar Habasha.
A yau talata hukumomin Habasha suka bayyana cewar, zaftarewa kasa a wasu yankunan kasar masu nisa sakamakon mamakon ruwan sama ta hallaka akalla mutane 157.
Kungiyar likitoci ta kasa da kasa Medecins Sans Frontieres (Doctors Without Borders - MSF) ta ce fararen hula a Sudan suna fuskantar munanan tashe-tashen hankula a cikin sama da shekara guda da aka kwashe an gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun sa-kai masu adawa da juna.
Shugaban kasar Sudan Abdel Fattah al-Burhan, ya karbi bakuncin jakadan Iran ranar Lahadi ya kuma tura nasa zuwa Tehran, a cewar gwamnatin kasar, don sake kulla dangantaka tsakanin kasashen shekaru takwas bayan tabarbarewarta.
‘Yan bindiga sun kai hari a kan iyakar Nijar da Najeriya, inda suka kashe mutane biyar tare da jikkata wani daya a garin Dambu da ke karamar hukumar Bazaga ta gundumar Birni N'Konni, sannan suka sace dabbobi da dama a garin.
Domin Kari