Kasar Mali, inda hukumomin soji suka kwace mulki a wani juyin mulki a shekarar 2020 da 2021, na fama da tashe-tashen hankula na masu kishin Islama na tsawon shekaru.
Ta ce sojojin na Rasha ba sojojin haya na Wagner ba ne, amma masu horar da sojoji ne da ke taimaka wa sojojin cikin gida da kayan aiki da aka sayo daga Rasha.
Kungiyar 'yan tawayen, mai suna Permanent Strategic Framework for Peace, Security and Development (CSP-PSD), ta fada a ranar Asabar cewa, ta kwace motoci sulke, da manyan motoci da tankokin yaki a yakin da aka yi a garin Tinzaouaten da ke kan iyaka.
Wagner ta ce "a ranar farko, kungiyar 'Pond group' ta lalata yawancin masu kishin Islama tare da sanya sauran tserewa," in ji Wagner a Telegram.
"Duk da haka, wata guguwar rairayi da ta biyo baya ta bai wa masu tsattsauran ra'ayi damar sake hada kai tare da kara yawansu zuwa mutane 1,000.
Wagner ta ce mayakanta sun sake kare wani harin da aka kai musu amma a karkashin wata gagarumar wuta da 'yan tawaye suka yi, an samu asarar rayuka a tsakanin Wagner da sojojin Mali.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna