Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Daukar Matakan Yaki Da Cutar HIV/SIDA A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya


Gwajin HIV/AIDS
Gwajin HIV/AIDS

Wani sabon rahoto ya bayyana cewa kimanin mutane miliyan 1.3 ne suka kamu da cutar HIV mai karya garkuwar jiki a shekarar 2023, inda da yawa daga cikin wadanda suke fama da cutar ke a nahiyar Afirka, a cewar hukumar UNAIDS.

Rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke yaki da cutar AIDS ko SIDA na shekarar 2024, wanda aka fidda a lokacin taron yaki da cutar ta SIDA na duniya da aka yi a bana, ya nuna cewa mutane miliyan 30.7 da ke dauke da cutar HIV ke shan magani yanzu haka. An samu raguwar mace-mace masu alaka da cutar SIDA da kashi 69 cikin 100 tun bayan da cutar ta yi tsanani a shekarar 2004, haka kuma an samu raguwar mace-macen da kashi 51 cikin 100 tun daga shekarar 2010. Bayanan rahoton sun nuna cewa an samu ci gaba wajen ba masu dauke da cutar damar samun magani da kuma raguwar mace-mace.

"Bayanai sun nuna an samu ci gaba. Shekaru tara da suka gabata, kashi 47 cikin 100 na masu dauke da kwayar cutar HIV ne kadai ke karbar magani. A yau adadin ya kai kashi 77 cikin 100. Hakan na nufin an samu karuwar kashi 30 cikin 100 na masu fama da cutar da ke samun magani a cikin shekaru 9 da suka wuce. Amma har yanzu kasashen duniya basu hau hanyar kawo karshen cutar SIDA nan da shekarar 2030 ba. A cikin kowanne minti daya ana samun mutum daya da ke mutuwa sakamakon rashin lafiyar da ke da nasaba da HIV. Har yanzu annoba ce. Hanyar magance matsalar daya ita ce daukar matakan da suka dace. Hukumar yaki da cutar HIV ta duniya na bukatar dala biliyan 9.5. Wannan gibin da aka samu na karuwa," a cewar Winnie Byanyima babbar daraktar hukumar UNAIDS.

Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS)
Majalisar Dinkin Duniya kan cutar kanjamau (UNAIDS)

Hukumar UNAIDS ta ba da rahoton cewa kusan rabin sabbin masu kamuwa da cutar HIV a shekarar 2023 na a gabashi da kudancin nahiyar Afirka, yayin da ake da kashi 15 cikin 100 a yammaci da tsakiyar Afirka. A shekarar, yara 120,000 suka kamu da cutar, kuma 76,000 suka mutu sakamakon rashin lafiyar da ke da nasaba da SIDA. An dai fara daukar matakan wayar da kan jama'a a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

“Ni maraya ne, ni kadai a cikin ‘yan’uwa uku ke shan magani a duk rana kuma ina shan maganin ba fasawa, ina dauke da kwayar cutar HIV tun lokacin da aka haife ni, fiye da sau daya, na yi kokarin kashe kaina ta hanyar shan magunguna," a cewar Gniwali Ndangou.

Masu lura da lamura sun ce yaki da kuma talauci su suka ta'azzara kalubalen da ake fuskanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Haka kuma rashin samun daidaiton jinsi na kara tsananta hadarin kamuwa da cutar HIV.

Kwayar cutar HIV
Kwayar cutar HIV

"Rashin daidaito tsakanin jinsi da cin zarafin mata sun sa mata a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya cikin hadarin kamuwa da cutar HIV, musamman a tsakanin masu shekaru daga 20-24," a cewar Chris Fontaine, Daraktan hukumar UNAIDS a kasar.

Cibiyoyin ba da tallafi kamar na CISJEU na taka muhimmiyar rawa wajen dakile yaduwar cutar da fadakarwa.

"CISJEU cibiya ce ta matasa, wadda ke yin ayyuka da yawa kamar samar da kariya da wayar da kan jama'a da kuma jinya kamar yadda ake bukata a al'umma don kuma al'ummar. Mun kuma dauki ma’akata 160 tare da horar da su, 80 a makarantu sauran 80 din kuma a cibiyoyin matasa," a cewar Michael Guéret, jami'i a cibiyar CISJEU.

A karon farko a tarihi tun bayan bullar annobar HIV/SIDA a duniya, yawan masu kamuwa da kwayar cutar HIV a yankin kudu da hamadar Sahara ya ragu ainun. Yayin da aka samu gagarumin ci gaba a yaki da cutar HIV/SIDA, sabon rahoton hukumar ta UNAIDS ya jaddada bukatar kara samar da kudade da kuma samun hanyoyin samar da magani cikin gaggawa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG