Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta bada sanarwar rage farashin man fetur da na diesel da nufin rage wa al’umma radadin tsadar rayuwa.
A wani samamen kasa da kasa da ya maida hankali akan kungiyoyin batagarin dake aikata laifuffuka a nahiyoyi 5 masu tushe a kasashen yammacin Afrika, ‘yan sanda sun kama mutane 300 sun kwace tsabar kudi dala miliyan 3 da toshe asusun banki 720, a cewar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.
Ruftawar wata haramtacciyar mahakar zinariya tare da birne mahakan da ransu ya hallaka akalla mutane 5 a arewacin kasar kenya, a cewar hukumomin yankin.
Yayinda al’ummar Musulmi a kasashe daban daban ke shagulgulan sallar Ashura a yau talata 10 ga watan Muharram, ‘yan shi’ah sun yi tattaki a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar domin nuna juyayi akan kisan Imam Hussein, daya daga cikin jikokin annabi Muhammad S.A.W. da aka yi a Karbala dake kasar Iraqi.
Malawi ta sanar da cewa, ta kawo karshen barkewar cutar kwalara mafi muni a kasar, cutar da ta kashe kusan mutane 2,000 tun bayan bullar ta a watan Maris din shekarar 2022.
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 99% na kuri'un da aka kada, a cewar sakamakon zaben farko - kashi 79% na kuri'un da aka kada - wanda hukumar zaben kasar ta fitar da yammacin jiya Litinin.
‘Yan sanda sun ce an kashe mutane biyar wasu ashirin kuma sun jikkata a harin da aka kai birnin Mogadishu.
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun karfafa matakan tsaro a gundumar Tilabery da nufin farautar fursunonin da suka arce a ranar Alhamis da la’asar daga gidan yarin Koutoukale mai tazarar kilomita 50 daga babban birnin Yamai.
Wata kotun yanki a Afrika ta yanke hukuncin cewa, hukumomin Najeriya sun take hakkin masu zanga zanga, a yayin gagarumar zanga zangar kin jinin cin zalin da yan sanda keyi, a shekarar 2020.
Ma’aikatar cikin gida ta jamhuriyar Nijar tace ta bada umurni ga bangarorin jami’an tsaro dabam dabam domin kasancewa cikin shirin ko ta kwana, bayan da fursunoni su ka arce daga gidan kaso mai tsaron gaske na Koutoukale, da fursunonin da ke ciki suka hada da mayakan kungiyar jihadin Musulunci.
A yau Alhamis Shugaba William Ruto na kasar Kenya ya sallami kusan dukkanin ministocinsa sannan ya sha alwashin kafa sabuwar gwamnati da za ta kunshi mambobi kalilan tare da aiki yadda ya dace sakamakon makonni da aka shafe ana zanga-zangar adawa da karin haraji da rashin iya mulki.
Domin Kari