Yayin da kasar Amurka ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa aranar Talata, 5 ga watan Nuwamba 2024, sauran kasashen duniya na sa ido sosai, har da kasar Ghana domin irin tasirin da zaben zai yi a kasashe masu tasowa musamman kuma da irin kawancen da ke tsakanin Amurka da Ghana
A kokarin tabbatar da adalci da karfafa yardan jama’a, hukumar zaben Ghana ta gayyaci ‘yan jarida da su sanya ido a kan yadda ake buga takardun zabe a kamfanoni uku daga cikin shida da aka kebe domin buga takardun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 7 ga watan Disamba
A yau ne kamfanin Orano na kasar Faransa ya sanar da dakatar da aikin hakar karfen Uranium a Jamhuriyar Nijar da sojoji suke mulki kusan watanni goma sha biyar.
Shugaba William Ruto ya zabi Ministan Harkokin Cikin Gida, Kithure Kindiki, domin maye gurbin Gachagua, wanda lauyoyinsa suka kalubalanci wannan zabin.
Sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da Ghana ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Disambar 2024.
Kungiyar ‘yan tawayen sudan ta RSF da kawayenta sun aikata munanan laifuffukan cin zarafi ta hanyar lalata, inda suka rika yiwa farar hula fyade yayin da dakarunsu ke garkuwa da mata a matsayin kwarkwarorinsu a tsawon watanni 18 da aka shafe ana gwabza yaki, a cewar wani jakadan MDD a yau Talata
Yakin na Sudan ya shafi miliyoyin mutane ta fuskar raba su da muhallansu, haddasa karancin abinci da salwantar da rayukan jama'a da dama.
Gwamnatin mulkin sojan kasar Jamhuriyar Nijar ta cimma wata yarjejeniyar kafa wata sabuwar matatar mai da kamfanin Zimar na Canada da nufin samar da wadatar man fetur da iskar gas a kasar da na kasuwanci.
Sanarwar da fadar shugaban kasar Chadin ta fitar tace an kai harin ne kusa da garin Ngouboua dake shiyar yammacin kasar, “inda ya hallaka kimanin mutane 40.”
Rasuwar Hama Amadou da ke matsayin tamkar wani abin ba zata ta matukar girgiza jama’a inda hatta ‘yan siyasar da suka sha karawa da shi a fagen siyasa sun nuna alhini kan mutuwarsa, suna masu kwatanta abin a matsayin babbar asara ga kasa.
A bara ne Amadou da ke hijira a kasashen waje ya koma gida da nufin ba da gudunmowa a kokarin fitar da kasar daga dambarwar siyasar da ta biyo bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023.
Domin Kari
No media source currently available