Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Ghana Ta Gayyaci 'Yan Jarida Su Sanya Ido Kan Buga Takardar Zabe


Mataimakin shugaban Hukumar Zaben Kasar Ghana, Bossman Asare
Mataimakin shugaban Hukumar Zaben Kasar Ghana, Bossman Asare

A kokarin tabbatar da adalci da karfafa yardan jama’a, hukumar zaben Ghana ta gayyaci ‘yan jarida da su sanya ido a kan yadda ake buga takardun zabe a kamfanoni uku daga cikin shida da aka kebe domin buga takardun zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki na ranar 7 ga watan Disamba

Kamfanonin uku da ‘yan jaridan za su je sun hada Inolink Printing Limited, Buck Press, da kuma Acts Commercial.

Dokta Benjamin Bannor-Bio, darakta mai kula da harkokin zabe na hukumar zabe ta EC, ya bayyana cewa, a halin yanzu ana buga takardun kuri’a na ‘yan majalisa ne saboda an dakatar da buga takardar zaben shugaban kasa na wani dan lokaci zuwa tsawon kwanaki 10 saboda rasuwar Akua Donkor, ‘yar takarar jam’iyyar Ghana Freedom Party.

Ya kuma jaddada cewa, tsarin buga takardun zaben a bayyane yake, da kuma hadin gwiwa da wakilan jam’iyyun siyasa a kowane mataki don tantance bayanai, kamar sanin lamba ta nawa da kuma sanin adadin da kowace mazaba ke bukata.

"Idan muka ce gaskiya da rikon amana na gudana, ba kawai muna fada bane, amma muna nufin hakan. Hukumar zaben Ghana na daya daga cikin hukumomin zabe kalilan a yankin Afrika ta Yamma da ke buga takardun zabe a kasar, kuma Buck Press na daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a harkar buga takardar zabe. A wannan babban zaben 2024, Buck Press ne zai buga takardu na yankuna hudu da suka hada da Ashanti, Oti, Savanna da kuma yankin Tsakiyar kasar.

“Mun zo nan ne domin mu sanar da ku cewa ba a bugun takardun zaben a asirce. Muna ba wa jama’a damar ganin yanda ake aiki, kuma muna yin hakan tare da wakilan jam'iyyun siyasa. A kowane mataki, waɗannan wakilai suna nan kuma suna lura don tabbatar da cewa an yi abin da ya dace.

"Suna lura da jerin lambobin takardun, suna lura da adadin da ake buga wa kowace mazaba kuma muna ba su duk wadannan cikakkun bayanai," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa, “Baya ga makullin hukumar zabe, su ma suna kara makullansu suna kuma daukar bayanan irin haka. Don haka, wajen buga takardar zabe, babu wani sirri, ana gudanar da komai a fili ne.”

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG