Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Koriya ta Kudu Yayi Murabus


​Fadar Shugabar Koriya Ta Kudu Park Geun-Hye ta ce Shugabar za ta amince da murabus din Firayim Minista, to amma sai an shawo kan matsalolin da su ka biyo bayan hatsarin jirgin ruwan Sewol.

Firayim Minista Chung Hong-won ya gabatar da takardar murabus dinsa da safiyar yau Lahadi, sanadiyya irin yadda jama'a su ka nuna rashin jin dadinsu da matakan da gwamnatinsa ta dauka, game da hatsarin jirgin ruwan na ran 16 ga watan nan na Afrilu, da ya yi sanadin mutuwa ko bacewar mutane sama da 300.

Mr. Chung wanda ke cikin alamar zullumi, ya sanar da murabus dinsa ne a wani jawabin da aka yada ta gidan talabijin da safiyar yau dinnan Lahadi, inda ya ce "cigaba da zama na a wannan mukamin wani babban dauyi ne ga wannan gwamnatin." Da ma a kasar Koriya matsayin Firayim Minista na je ka na yi ka ne. Shugaban kasa ne ke da akasarin ikon.

Shi dai wannan jirgin ruwan mai nauyin ton 6,800 mai suna Sewol na dauke ne da daruruwan 'yan makaranta da malamansu da ke kan hanyarsu ta ziyartar tsibirin Jeju da ke Kudu maso yammacin kasar, yayayin da ya yi hatsari ya nitse.
XS
SM
MD
LG