An bukaci a kara jami'an tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya domin cimma burin tsaro a wannan yanki.
Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bada sanarwar sako fursunoni siyasa hudu wandanda aka zarga da yunkurin juyin mulki, a wani yunkuri na farfado da hawa kan teburin shawarwari da masu adawa.
Yau ne ranar da hukumar lafiya ta duniya ta ware domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro a duk fadin duniya.
Yau ake bukin cika shekaru goma sha tara da gwamnatin kasar Nijer da ‘yan tawayen Azbinawa dake fafutukar aware domin neman yancin cin gashin kan arewacin kasar.
Iyayen daliban da aka sace a Makarantar Sakandare dake Cibok a jihar Borno sun yi taro inda suka yi kira ga 'yan ta'adda dasu sako 'ya'yan nasu su sama da 200 da aka sace.
Mahukuntan kasar Yemen sun tabbatar cewa 'yan ta'ada masu alaka da kungiyar al-Qaida sun kashe jami'an tsarota guda hudu
Kimanin mutane dubu ashirin da biyar ne tare da tsohon ministan yada labarai Ikra Aliyu suka canza sheka daga jamiyar PDP zuwa ta APC a wani gangami a Gusau.
Sarakuna na da daraja ta musamman da ake ganin kimarsu, kuma suna da rawar takawa dangane da tsaron al-ummomin Najeriya.
An kamo wani mutum da ake Zargi da yan-yanka wata yarinka gunduwa-gunduwa domin yin kudi.
Bayan fashewar bama-bamai a Nyanya kusa da Abuja da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu da yawa, jami'an tsaron Najeriya sun tsananta tsaro da biniken kwakwaf na ababen hawa
Akalla mutane talatin da shida suka mutu yayin da wata mota kiya-kiya ta afkawa motar daukan kaya a kasar Mexico
A wata gobara mai muni a kasar Chile akalla mutane goma sha shida suka rasa rayukansu. Idan ba'a manta ba kwanan nan kasar tayi fama da girgizar kasa.
Domin Kari