Babban kotun tarayya dake Abuja, ta yanke hukuncin tsoffafin ‘yan majalisar tarayyar nan na PDP 37, da sukayi sauyin sheka zuwa jam’iyyar adawa ta APC, su ajje kujerunsu, su bar majalisar.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai isa kasar Isira'ila a yau domin tattaunawar diflomasiyyar zaman lafiya da Falasdinawa
Firayim Ministan Rasha Dmitry Medvedev na yankin Crimea. Shi ne mafi babban mukami cikin jami'an Rasha da su ka je Crimea tun bayan da Rashar ta karbe yankin daga Ukraine a farkon wannan watan.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi Ahmed Muazu ya zama sabon shugaban jam'iyar PDP,
Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius yace Iran da giggan kasashen duniya guda shidda sun cimma matakin farko na yarjejeniyar kayade shirin nukiliyar Iran, ita kuma a sausauta takunkunmi da aka aza mata.
'Yan kasuwa sun fara yin tururuwa su na zuwa birnin Mogadishu
Hukumomin kasar Kenya na ci gaba da kokarin neman kama maharan da ke boye a cikin Westgate Mall
Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, da takwaran aikinsa na Rasha, Sergei Lavrov, su na wani sabon yunkurin gudanar da taron neman zaman lafiya da aka jima ana jinkirtawa da nufin kawo karshen yakin basasar kasar Sham, ko Siriya.
Daruruwan al-umma sun yi dafifi domin nuna farin cikinsu bisa haifan da na miji, da mai dakin Yarima Williams tayi ran Litinin dinnan.
Sojoji sun hambarar da shugaban demokradiyya na farko a kasar Masar, kuma sun rantsar da shugaban rikon kwarya yau kwana daya kennan, kuma wannan lamari, ya samu tsokaci iri-iri daga manazarta da kwararru a harkokin siyasa.
A Nijar-rikicin jam'iyar CDS bangaren mahaman usman yace zai daukaka kara a gaban kotun CEDEAO ko ECOWAS.
Domin Kari