Iyayen daliban da aka sace a Makarantar Sakandare dake Cibok a jihar Borno sun yi taro inda suka yi kira ga 'yan ta'adda dasu sako 'ya'yan nasu su sama da 200 da aka sace.
Mahukuntan kasar Yemen sun tabbatar cewa 'yan ta'ada masu alaka da kungiyar al-Qaida sun kashe jami'an tsarota guda hudu
Kimanin mutane dubu ashirin da biyar ne tare da tsohon ministan yada labarai Ikra Aliyu suka canza sheka daga jamiyar PDP zuwa ta APC a wani gangami a Gusau.
Sarakuna na da daraja ta musamman da ake ganin kimarsu, kuma suna da rawar takawa dangane da tsaron al-ummomin Najeriya.
An kamo wani mutum da ake Zargi da yan-yanka wata yarinka gunduwa-gunduwa domin yin kudi.
Bayan fashewar bama-bamai a Nyanya kusa da Abuja da suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma raunata wasu da yawa, jami'an tsaron Najeriya sun tsananta tsaro da biniken kwakwaf na ababen hawa
Akalla mutane talatin da shida suka mutu yayin da wata mota kiya-kiya ta afkawa motar daukan kaya a kasar Mexico
A wata gobara mai muni a kasar Chile akalla mutane goma sha shida suka rasa rayukansu. Idan ba'a manta ba kwanan nan kasar tayi fama da girgizar kasa.
Yayin da ake cigaba da kirga kuri'u a zaben da aka yi a kasar Afghanistan mutane biyu suna kan gaba lamarin da ka iya kaiga zagaye na biyu
Yayin da kasashen yammacin turai ke cigaba da zargin Rasha da haddasa borin da wasu keyi a kasar Ukraine, gwamnatin kasar tace zata murkushe 'yan tawayen Jumma'annan.
Jami’an kasar Afghanistan sunce wani dan sanda ya harbe wasu mata ‘yan jaridar kasashen ketare su biyu, inda ya kashe daya sannan ya ji wa dayar rauni, gabannin zaben shugaban kasa.
Jami’an Mali na binciken barkewar cutar da ake zaton zazzabin Ebola ne, bayan barkewar cutar a wannan yanki.
Domin Kari