Malamai suna da muhimmanci wajen kawo cigaban rayuwa, ba kawai don koyar da karatu da rubutu ba, har ma da koyar da kimiyya da fasaha da sauran bangarorin rayuwa.
Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA ta bukaci al’umma su kai rahoto wa hukumomi duk wata alamar barazana ta muhalli, don kare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.
Ministan harkokin noma da raya karkara, Muhammad Mahmood Abubakar ya bayyana hakan a taron koli na masu ruwa da tsaki a harkar noma, karo na arba’in da biyar, da aka gudanar a Jos, a fadar Jihar Filato.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa Mr. Dan Manjang ya ce ba su ji dadin hukuncin kotu ba.
Kotun sauraron kararrakin zabe a jihar Filato ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya (INEC) ta ayyana Muhammad Adam Alkali na jami'iyyar PRP a matsayin wanda ya lashe zaben kujerar majalisar wakilai ta Jos ta Arewa da Bassa.
Hukumomi a karamar hukumar Pankshin ta Jihar Filato, sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, ciki har da wata mace da mijinta, sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta auku a kauyukan Nyelleng da Gwabi.
Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta ce matasan da ta kama take tsare da su, tana tuhumarsu ne kan sha'anin tsaro.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yiwa tsohon gwamnan jihar Filato dake daure a gidan gyara hali afuwa.
A cikin ‘yan kwanakin nan, an sami ce-ce-kuce kan sake gina kasuwar, bayan da bankin Jaiz ya nemi yin yarjejeniya da gwamnatin jihar Filato don ya gina kasuwar cikin shekara daya.
Kimanin makarantu masu zaman kansu dubu biyar ne ke gudanar da harkokinsu ba tare da samun lasisi daga gwamnati ba a jihar Filato.
Yayin da matsalar tsaro ke kara ta’azzara a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, jihohin dake makwabtaka da birnin sun fara daukan matakan tsare rayukan al’ummarsu.
Al’ummomin wasu yankunan dake kananan hukumomin Wase da Kanam a Jahar Filato sun koka kan yadda ‘yan bindiga ke kisan mutane suna sace dabbobi da yin garkuwa da mutane a kauyukansu.
Maniyyata dubu daya da dari biyar ne basu sami tafiya aikin hajjin bana ba, da suka hada da mutane tara daga Jahar Bauchi, mutane tasa’in da daya daga Jahar Filato da wassu dari bakwai daga Jahar Kano.
Bayan kammala zabubbukan fidda gwani da jami’iyyun siyasa a Najeriya suka yi, al’ummar kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu kan bukatun da suke so wadanda suka sami shugabanci a zaben shekara ta dubu biyu da ishirin da uku, su fuskanta, don kawo sauyi mai inganci a rayuwarsu.
Yayin da shekara ta 2023 ke kara karatowa, ‘yan siyasa na ta fafutikar neman hawa kujerun madafun iko a zabukan da za’a gudanar badi, babban kalubale da Najeriya ke fuskanta shi ne na tsaro.
Wasu ‘yan majalisar karamar hukumar Mangu a Jahar Filato sun tsige mataimakin shugaban karamar hukumar, Alhaji Garba Hassan suka kuma dakatar da shugaban karamar hukumar, Daput Minister Daniel na tsawon watanni uku.
Sakataren majami’ar ECWA, Rabaran Yunusa Nmadu ya shaida wa Muryar Amurka cewa ECWA, da ma sauran kungiyoyin addinin Kirista ba sa tilasta mutum shiga addinin, ba tare da amincewarsa ba.
A tsarin dimokradiyya, matsayin mataimakin shugaban kasa na da muhimmanci kamar na shugaban kasa, saboda shine ke rike shugabancin kasar, yayinda shugaban kasar ya shiga wani yanayi, ko dai na rashin lafiya, ko yayi murabus, ko ya rasu.
Bayan kammala zabubbukan fidda ‘yan takara da za su kara a zaben gama gari na shekarar 2023, hankalin jama’a yanzu ya karkata kan wadanda jam’iyyun zasu zaba a matsayin mataimakan shugaban kasa.
Kungiyar mambobin Katolika a Najeriya ta bukaci hukumomi su zakulo su kuma hukunta wadanda suka kashe masu ibada a majami’ar Saint Francis dake Owo a Jahar Ondo.
Domin Kari