Tun farko dai hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan Filato Joshua Dariye gaban kotu, bayan da ta zarge shi da yim sama da fadi da sama da Naira Biliyan daya da miliyan 16.
A shekarar 2018 kotu ta yankewa Joshua Dariye hukuncin daurin shekaru 14 kan laifin cin amana, sai kuma karin wasu shekaru biyu kan laifin yin almubazzaranci da dukiyar al’umma.
Barista Isyaku Barau mai sharhi kan lamura, ya ce dokar kasa ta baiwa shugaban kasa hurumin yiwa duk wani fursuna da ake tsare da shi bisa ko wanne irin laifi afuwa.
Baya ga Joshua, shugaba Muhammad Buhari ya yiwa tsohon gwamnan jihar Taraba Jolly Nyame da sauran wasu fursinoni har 150 afuwa.
Yayin da kotu ta umurci tsohon gwamnan na Jahar Filato, Joshua Dariye ya mayar wa gwamnatin Jahar Filato da Naira miliyan 80 da hukumar EFCC ta bankado
Sashen Hausa ya ji ra’ayoyin wasu ‘yan jihar Filato kan wannan labari na yafewa tsohon gwamnan da Buhari ya yi. Yayin da wasu ke ci gaba da murna da maraba da shi, wasu kuwa na ganin yin hakan bai dace ba.
Saurari rahotan Zainab Babaji don Karin bayani.