A Jahar Filato, wasu da muryar Amurka ta zanta da su sun bayyana cewa harkokin ilimi, rashin ayyukan yi, matsalolin shaye-shaye da inganta rayuwar al’umma na daga cikin dimbin bukatu na gaggawa da gwamna da zai karbi mulki zai magance.
Malama Bilkisu Umar tace suna bukatar ‘ya’yansu su sami ilimi mai inganci don tallafa wa kansu da zuri’ar su.
Jabir Abdulrazak yace rashin aikin yi ya sanya wassu matasa shiga shaye-shaye da wassu harkoki marasa fai’ida
Barista Caleb Mutfwang dake takarar gwamnan Jahar Filato a jami’iyyar PDP yace zai magance matsalolin tsaro don samar da kayayyakin more rayuwa ga al’umma.
Shima ‘dan takarar gwamnan Jahar Filato a APC, Farfesa Nentawe Yilwatda yace zai kafa gidauniya don samun kudaden da zai magance rashin tsaro da samadda ci gaba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: