Kididdiga, lissafi da kuma ikirari iri iri na dada jefa ayar tambaya kan ko wa zai zama Shugaban Amurka na gaba.
Masu zanga zanga sun fito a garuruwa da dama jiya Laraba don kiran da a kammala kirga kuri’un zaben shugaban Amurka.
An zaku a samu sakamakon zaben Shugaban kasar Amurka, amma ganin yadda aka kada kuri'u da dama ta hanyar aikewa da wasiku, an samu jinkiri wajen kammala kidayar wasu muhimman jahohi, wadanda sakamakonsu ne zai nuna alkibar zaben.
Kamar yadda al'amarin yake a duk inda aka kammala zaben Shugaban kasa amma sakamakon karshe ya kasa samuwa cikin lokaci, Amurkawa sun zaku su san makomar zaben da su ka yi.
Kamar sauran kasashe a fadin duniya, annobar corona ta janyo ma Najeriya asarar biliyoyin Naira, wanda hakan ke barazana ga tattalin arzikinta.
Yawan gallaza ma jama'a da ake zargin 'yan sanda na musamman da ake kira SARS da yi, ya sa wasu matasa yin zanga zanga a gaban ginin shelkwatar ‘yan sanda da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja.
Tsohon dan takarar shugaban kasar Mali Soumaila Cisse ya gana da shugaban rikon kwaryar kasar a daren ranar Alhamis 8 ga watan Oktoba karon farko tun bayan sakinsa a wannan makon da masu kaifin kishin Islama suka yi a wata musayar fursunoni.
Yayin da dalibai su ka koma makaranta da tsarin karatu kusan irin wanda aka saba da shi, masu lura da al'amura na ganin da alamar ba a dau ingantattun matakan kare dalibai ba a jahar Kebbi.
Yayin da masu kai ziyarar ibada ta mabiya tafarkin Mouride ke ta dunguma zuwa birni mai tsarki na Touba a kasar Senegal don ayyukan ibada na Magal, hukumomi na damuwa kan yiwuwar hakan ya yada cutar corona.
Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 120, da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 05 ga watan Oktoba.
Bayanai na nuna cewa rashin cancantar daliban jahar Kano ta Najeriya ya haifar da tafiyar hawainiya ga kwalejin gamayya ta Jamhuriyar Nijar da jahar Kano ta Najeriya.
A cigaba da rigimar da ta biyo bayan wasu kalaman da tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya ya yi game da matsalar tsaro a Kudancin Kaduna, wata kotu a Jos ta tabbatar da hurumin hukumar 'yan sandan da ta gayyace shi
Amurkawa sama da miliyan 100 ake kyautata zaton za su kalli muhawarar farko tsakanin Shugaba Donald Trump na jam'iyyar Republican da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Joe Biden na Jam'iyyar Demokarat.
Wata sabuwa kuma ta kunno kai game da takarar sanannen dan adawar Jamhuriyar Nijer dinnan, Hama Amadou. Wannan karon takaddama ake yi kan rashin rajistarsa.
Jama'a sun yi cincirindo tare da daukar matakan kandagarki a wurin nadin sabon Sarkin Biu, Mai Martaba Mustafa Umar Mustafa.
Domin Kari