NIAMEY, NIGER - Yanayin tsaro a yankin Sahel abu ne da ya kamata a samu canjin al’amura, wannan shi ne abinda Majalisar Dinkin Duniya ta kudirta a watannin baya ta hanyar wasu jerin matakai da aka dauka don fitar da farar hula daga kangin da suka tsinci kansu ciki a yankin sanadiyar lalacewar al’amuran tsaro, mafari kenan aka bukaci wasu kungiyoyin farar hula kimanin 50 na Coalition Citoyenne pour le Sahel daga kasashen Nijer, Burkina Faso, da Mali su gudanar da bincike domin tantance halin da ake ciki bayan zartar da shawarwarin da aka bayar a can baya.
Shugabar kungiyar APAISE Niger Rabi’a Djibo Magaji, ita ce ta gabatar da rahoton wannan bincike a gaban taron Majalisar Dinkin Duniya a bisa gayyatar kasar Brazil mai shugabancin kwamitin sulhun a watan nan na Yuli. Ta ce ba a samu sauyi ba sosai a baya bayan nan kuma bincike ya gano cewa a duk rana ana kashe kimanin mutun 8 a yankin Sahel sakamakon harin ta’addanci, kuma ya kamata a sa mata a zaman shawarwarin da ake yi tunda su da yara kanana suka fi dandana kudarsa a lokutan tashin hankali.
Binciken ya kuma gano cewa an samu lafawar cin zarafi da kisan da a ke zargin jami’an tsaro da yi wa farar hula wadanda ba su ji ba su gani ba.
A jerin shawarwarin kungiyoyin na Coalition Citoyenne sun gargadi gwamnatocin kasashen da su bi hanyoyin lalubo mafitar rikicin ta’addanci da ke ci gaba da tsananta a wannan yanki.
Da ma a kwanakin baya wasu kungiyoyin kare hakkin mata sun koka a game da yadda ‘yan bindiga ke cin zarafin farar hula musamman mata a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, yayin da a wani zubin baragurbin jami’an tsaro ke aikata abubuwan da basu dace da aikinsu na wadanda ke da alhakin bai wa jama’a kariya ba.
Saurari rahoton Souley Mumuni Barma: