A yayinda wa’adin rufe iyakokin kasar Saudiyya ke cika a yau Laraba, 6 ga watan Yuli , Hukumar Alhazzan Jamhuriyar Nijer ta ce ta samu Karin wa’adi don kammala ayyukan jigilar wasu maniyyatan kasar sama da 1000 da ke birnin Yamai suna jiran zuwan jiragen da za su kwashe su.
Koda yake akwai alamun samun ci gaba akan maganar jigilar alhazzan Jamhuriyar Nijer idan aka kwatanta da kwanakin baya, hankulan maniyyata ya tashi sakamakon lura da tafiyar hawainiyar da ake fuskanta wajen gudanar da wannan aiki, a yayin da ake gab da rufe iyakokin Kasa Mai Tsarkin. To amma a cewar shugaban Hukumar Alhazzai ta COHO, Alhaji Ibrahim Kaigama, hukumomin Saudiyya sun bai wa Nijer izinin ci gaba da ayyukan jigila har zuwa sha biyun daren gobe Alhamis.
Baya ga halin rashin tabbas din da aka shiga sanadiyyar karancin jirage, maganar Visa, ita ma wata matsala ce da ta shafi wasu tarin maniyyata, lamarin da ake dora alhakin faruwarsa a wuyan shugaban hukumar ta COHO. Sai dai Commmissaire Kaigama yace wannan batu ne dake tsakanin alhazzai da kamfanonin aikin Hajji da Umara.
Yanzu dai kallo ya koma filin jirgin saman Diori Hamani dake nan birnin Yamai don ganin yadda za ta kaya game da makomar maniyyata 1358 din da ke jiran zuwan jirage a tsakanin yau Laraba zuwa gobe Alhamis, wa’adin karshe a yayin da alhazzan da suka riga suka sauka Kasa Mai Tsarki ke hawan Arfa a ranar Juma’a, 8 ga ta watan Yulin 2022, wato 9 ga watan Zul Hijjah, shekarar 1443 bayan hijira.
Saurari cikakken rahoton Suleiman Barma: