Dubun wani dan fashi ya cika a Jamhuriyar Nijar bayan da ya kai hari a wata ma’aikatar aika sakwannin kudade a birnin Yamai.
Masu ruwa da tsaki a kasuwanci da noman zogale sun fara wani zama don nazarin hanyoyin saka tsari a wannan fanni da ke samar da kudaden shiga ga dimbin ‘yan kasar musamman mata.
Shugaba Mohamed Bazoum ne ya jagoranci taron karrama mamacin, wanda ya rasu a ranar Litinin din da ta gabata, a fadarsa kafin a wuce da gawarsa zuwa makwancin karshe a garinsa na haifuwa wato Kornaka da ke Jihar Maradi.
Hukumar kididdigar jamhuriyar Nijer ta bayyana gano raguwar haifuwa a kasar sakamakon yadda jama’a su ka fara amincewa da matakan tsarin iyali.
Fitaccen dan sisayar kuma dan gwagwarmaya ya rasu ne jiya Litinin 18 ga watan Yuli a Asibitin Kwararru dake birnin Yamai, inda aka kwantar da shi a karshen makon da ya gabata don jinya.
Allah ya yiwa shugaban jam'iyar PNA Al'umma Sanoussi Jackou cikawa a yammacin jiya litinin a asibitin kwararru na Birnin Yamai.
Hukumomin Jamhuriyar Nijer sun yi Allah wadai da yadda Russia ta yi fatali da dokokin kasa da kasa ta hanyar mamayar da ta yi wa kasar Ukraine.
Hukumomin Nijer sun yi tur da yadda Rasha ta yi watsi da dokokin kasa da kasa ta hanyar mamayar Ukraine, a cewarsu alama ce da ke nuna girman barazanar da kasashe masu karamin karfi ke fuskanta daga wadanda ke da ra’ayin amfani da karfin soja don cimma gurinsu.
Ministan tsaron Faransa da abokiyar aikinsa ta harakokin waje sun yi rangadi a Jamhuriyar Nijar inda aka tattauna akan batutuwan da suka hada da tsaro da ayyukan ci gaban al’umma a wani lokacin da rundunar Barkhane ke ci gab da kammala nade tarkacenta daga Mali zuwa jamhuriyar Nijar.
Kasashen Chadi da Nijar sun yi kiran Mali ta koma kan kujerarta a kungiyar G5 Sahel domin ci gaba da yakin hadin-gwiwar da takwarorinta ke kafsawa da kungiyoyin ta’addancin yankin Sahel.
Rundunar mayakan Jamhuriyar Nijar ta sanar cewa dakarun tsaro sun hallaka gomman ‘yan ta’adda a tare da wargaza ma’ajiyar kayayyakin ‘yan ta’adda a yammacin kasar banda wasu nasarorin da tace an samu a sauran yankunan dake fama da matsalolin tsaro.
Yayin da dumamar yanayi ke cigaba da illa a sassan duniya, wani taro da ake yi a Jamhuriyar Nijer zai yi bitar yadda abin ke shafar Afurka ta Yamma da kuma yadda za a dau matakin kare muhalli.
Yayin da kasashen Nijer da Benin ke fama da matsalar 'yan bindiga, makwabtan kasashen sun yanke shawarar hada karfi da karfe wajen tinkarar miyagun.
Wani bincike da aka gudanar a kasashen yankin Sahel wanda kuma aka gabatar da rahotonsa a taron kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya a karshen makon jiya ya gano cewa mata da yara kanana sun fi kowa dandana kuda a tashe tashen hankulan da ake fama da su.
Ma’aikatar kudin Jamhuriyar Nijar ta fitar da sakamakon wucin gadi na binciken da aka gudanar domin kididdige ma’aikatan gwamnatin kasar da nufin tantance halattattun ma’aikata da na bogi.
Duk da cikar wa'adin jigilar maniyyata aikin Hajji na bana a yau Laraba, ga dukkan alamu sauran maniyyatan Nijer sama da 1000 za su iya samun Hajjin saboda Saudiyya ta kara ma Nijer lokaci, a cewar hukumomi.
Jami’an kare hakkin jama’a da ‘yan rajin kare dimokradiya sun yi na’am da matakin dage takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba wa kasar Mali a washe garin juyin mulkin da ya kifar da shugaba Ibrahim Boubakar Keita daga karagar mulki.
A jamhuriyar Nijer wasu daga cikin maniyatan aikin Hajji sun fara komawa garuruwansu bayan la’akari da cewa zai yi wuya a kai su kasar Saudiya kafin ranar 6 ga watan Yuli, duk da cewa mahukuntan Nijer sun sha alwashin kwashe dukkan mutanen da suka samu takardar Visa.
A Jamhuriyar Nijar an shiga halin dambarwa bayan da majalisar addinin Islama a kasar ta ayyana ranar Lahadi 10 ga watan Yuli a matsayin ranar da za a yi bukukwan babbar sallar a maimakon ranar asabar.
Domin Kari