Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijer Ta Jaddada Aniyar Shimfida Tsarin Inshorar Manoma Daga Shekarar 2023


Wani mutum a gonarsa da fari suka yiwa barna.
Wani mutum a gonarsa da fari suka yiwa barna.

Gwamnatin jamhuriyar Nijer ta jaddada aniyar soma zartar da tsarin inshorar manoma a shekarar 2023 da nufin takaita dimbin asarar da bala’in ambaliya da sauran illolin canjin yanayi ke haddasa wa manoma, makiyaya da masintan kasar a wannan lokaci da tallafin masu hannu da shuni ke karanci.

NIAMEY, NIGER - Sama da million 40,000 na CFA ne aka kyasta cewa suna salwanta a kowace shekara a Nijer sanadiyyar ambaliyar ruwa ko sauran bala'o’in da ke afka wa gonaki, da filayen kiwo, da wuraren kamun kifi, lamarin da ke shafar miliyoyin mutane da galibinsu mazaunan karkara ne masu dogaro akan wadannan ayyuka. Dalili kenan gwamnatin wannan kasa ta fara hangen aiki da tsarin inshorar manoma kamar yadda abin yake a yanzu haka a kasashen Afrika da dama.

Ministan ayyukan jinkai na Nijer Alhaji Lawan Magaji ne ya bayyana hakan a wani taron manema labaran da kwamitin nazarin hanyoyin shimfida tsarin inshorar manoma ya kira.

Da yake magana da yawun kungiyar manoma da makiyaya ta Plate Forme Paysanne Djibo Bagna, kuma mamba a wannan kwamiti, ya fayyace irin alfanun da ke tattare da wannan tsari idan ya tabbata, yana mai cewa tsarin zai tallafa wa manoma su rage asara idan damina ba ta yi kyau ba.

Daukar inshora a kasashen Afrika musamman a Nijer wani tsari ne da mafi yawancin masu ababen hawa ke ganinsa tamkar na tilas don kauce wa haduwa da fushin hukuma, ba wai don kare kai daga asara ba.

To ko wane tabbaci kamfanonin inshora ke da shi kan cewa a wannan karon inshorar za ta amfani mai ita? Djibril Talatou, mamba a kawamitin inshorar manoma kuma shugaban kungiyar masu kamfanonin inshora, ya ce kasashe da yawa a Afrika sun gwada kuma suna ganin alfanun tsarin, a saboda haka don me Nijer baza ta bi sahu ba.

An dai bayyana cewa a yadda tafiya ta kama hanya akwai yiyuwar soma aiki da wannan tsari a shekarar 2023 .

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG