Wadanan jami’ai su kimanin 54 matasa ne da suka ci jarabawar da hukumomi suka tsara a shekarar 2020 da nufin samar wa ma’aikatar Douane ko Costum kwararrun da suka karanci fanin shara’a da na tattalin arziki da sha’anin haraji wadanda aka kai su makarantar manyan sojoji wato EFOFAN inda suka shafe watanni 3 suna daukan horo sai dai yau fiye da shekara 1 bayan haka shigar da su sahun ma’aikata ya faskara, mafari suka yi zaman dirshan a harabar ma’aikatar kudi ta kasa wato ministere des finances don tayar da mahukunta daga barci a cewar daya daga cikin jagororinsu, Boukar Moustapha yayin da ya ke bayyani wa manema labarai.
A baya hukumomi sun yi yunkurin soke jarabawar da a yayinta wadanan matasa suka yi nasara saboda zargin cuwa cuwa sai dai kotun raba gardama wato conseil d’etat tace ba kamshin gaskiya a wannan zargi saboda haka ta umurci a ba su damar kama aiki.
A washe garin hukuncin alkalin kotun ta Conseil d’etat shugaban kasa ya ba jami’ai umurnin yin biyayya ga matakin kotun.
Dokar kasar Nijar dai ta kayyade cewa bai dace ba sabbin jami’an Costum su wuce watanni 3 suna zaman jiran kama aiki bayan kammala horon soja.
Duk yunkurin neman jin ta bakin magatakardan ma’aikatar ministan kudi yayin hada wannan rahoton ya cimma tura.
Da yake bayyana ra’ayinsa a game da kiki kakar dake tattare da shirin shigar da wadanan matasa a sahun ma’aikatan Douane jami’in fafutika na gamayyar kungiyoyin fararen hula ta FSCN Abdou Elhadji Idi ya nuna takaici akan yadda dabi’ar bijirewa umurnin kotu ke kokarin samun gindin zama a Nijer.
Jarabawar neman aiki ko ta neman difloma ko ta neman shiga ajin gaba a makarantu abubuwa ne da a ‘yan shekarun nan ke gudana cikin yanayin dambarwa a Nijer, lamarin da ya sa gwamnatin kasar ta shigar da hukumar yaki da cin hanci ta HALCIA a sahun masu kula da tsare tsaren dukkan jarabawar da za a gudanar da sunan hukuma sai dai da alama wannan mataki na fuskantar turjiya.
Saurari rahoton a sauti: