Hadin gwiwar kungiyoyin fafutuka na Tournons La Page na Jamhuriyar Nijar ya shawarci daukacin kungiyoyi masu zaman kansu su fara aiki da tsari na kayyade wa’adin shugabanci.
Yau ake bukin tunawa da ranar Hausa ta duniya da nufin bunkasa harshen Hausa da al’adun bahaushe sakamakon lura da tasirin Hausa a zamantakewar al’umomin kasashen da ke amfani da ita a matsayin hanyar sadarwa da musanyar abubuwa da dama.
A yayin da farashin ababen masarufi ke kara tashi a Jamhuriyar Nijar kwamitin ministocin da ke kula da yaki da tsadar rayuwa ya kira taron manema labarai domin sanar da al’umma yunkurin da gwamnati ke yi don tunkarar wannan al’amarin.
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta gargadi direbobin tasi da masu manyan motocin jigila su mutunta dokar da ta kayyade kudin motocin haya ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
Masu motocin jigilar fasinja da masu motocin dakon kaya sun cimma wata yarjejeniya da hukumomin jamhuriyar Nijer don ganin karin farashin man diesel din da aka yi a kasar a makon jiya bai shafi kudin motocin haya ba.
Matakin na zuwa ne a wani lokacin da al’ummar ta Nijar ke fama da tsadar kayan abinci saboda haka kungiyoyin fafatukar ke cewa suna jiran su gani a kas domin ba zasu laminci dukkan wani matakin da zai kara wa talaka damuwa ba.
Yayin da 'yan Najeriya ke ta cece kuce kan kudin da aka sayo motocin da aka bai wa Nijar da su ke ganin akwai coge a ciki, su kuwa 'yan Nijar damuwa su ke yi kan yadda wannan al'amari ya zama abin rigima.
A karshen wani taron da suka gudanar don nazari akan matakin karin farashin man dizel da gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dauka a farkon makon nan, kungiyoyin kwadagon kasar sun yi watsi da abinda suka kira yunkurin jefa talakkawa cikin kuncin rayuwa.
Kamar yadda aka saba, bukukuwan zagayowar ranar samun 'yancin Nijar, sun hada da dashen itatuwa a sassan kasar da dama
Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya yi jawabi ga ‘yan kasar ta kafafen labarai a jajibirin samun bukin ranar samun 'yancin kan kasar, inda ya tabo batutuwa da dama.
Yayin da rundunar sojojin jamhuriyar Nijar ta cika sheka shekaru 62 da kafuwa, hukumomin kasar sun bayyana shirin kara yawan dakaru daga dubu 33 zuwa dubu 50 kafin zuwa shekarar 2025 don yakar kungiyoyin ta’addanci.
Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kara kudin man diesel a gidajen man kasar sakamakon dalilan da ta kira masu nasaba da yakin Ukraine.
Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi a Jamhuriyar Nijar ta kama wasu mutune dauke da kwayar da aka shigo da ita daga Indiya da nufin sayar da wani bangarenta a mahakar zinaren jihar Agadez yayinda ake hasashen yiyuwar shigar da dayan bangaren kasar Libya.
A Jamhuriyar Nijar, ma’aikatar agajin kasar ta gargadi jama’a da su gaggauta barin wuraren da ke kusa da magudanan ruwa domin riga kafin abubuwan da ka iya biyo bayan ruwan saman da ake tafkawa a ‘yan kwanakin nan a galibin yankunan kasar.
A jamhuriyar Nijer kamfanonin cikin gida masu hada hadar aika sakwannin kudade sun bayyana damuwa dangane da yadda ‘yan fashi da makami suka fara yawaita kai hare hare akan ma’aikatansu a sassan kasar.
Domin Kari