Ko da yake mahukuntan Burkina Fason ba su ambaci sunan wata kasa ba, masu sharhi a kan sha’anin tsaro na kwatanta abin a matsayin wata alamar kama hanyar juya wa Faransa Baya.
A yayin da yake gabatar da tsarin manufofin gwamnatinsa a zauren majalisar dokokin kasarsa ne Firam ministan Burkina Faso Maitre Apolllinaire Kyelem De Tambela ya bayyana damuwa a dangane da rashin samun dauki irin na Zahiri daga kasashen da ke kiran kansu aminan Burkina Faso a wani lokacin da ‘yan kasar ke dandana kudar aika- aikar kungiyoyin ta’addanci..
Yace "Burkina faso kawace ga kowace kasar dake son kawance da ita amma fa muna jiran ganin an yi hulda ta tsakani da Allah domin muna kyautata zaton akwai wasu aminnan da ke binmu da zuciya 2 saboda yadda aka zuba ido ana kallo kasarmu ta na fama da ta’addanci tun a shekarar 2015."
Ya kara da cewa, "Idan babu gamin bakin wadanda ke kiran kansu aminnanmu ina ne suke samun makamai da harsasai da man fetur da kudaden kashewa? Ya kasashen da suka mallaki na’urorin zamani irin na hango abokan gaba ba sa ba mu bayanai akan kai da kawon wadanan ‘yan ta’adda?"
Furicin firam ministan na Burkina Faso na zuwa ne kwanaki 2 bayan da masu zanga zanga suka yi yunkuriin afkawa ofishin jakadancin Faransa a birnin Ouagadougou da wani sansanin sojan Faransa kafin daga bisani jami’an tsaro su tarwatsa su.
A cewar mai sharhi akan sha’anin tsaro Abass Abdoul Moumouni wadanan Karin alamomi ne dake tattabatar da cewa, an doshi hanyar raba gari a tsakanin kasashen 2.
A tasa fahimta,r mai fashin baki kan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum na cewa, irin abubuwan dake wakana a halin yanzu wani al’amari ne da ya kamata gwamnatin Faransa ta dauke su da mahimmanci duk da cewa gwamnatocin wasu daga cikin kasashen Sahel na da rauni.
Shekaru a kalla 10 kenan da girke dakarun Faransa a yankin Sahel da sunan yaki da ta’addanci sai dai rashin gani a kasa ya sa al’ummomin wadanan kasashe fara zarginta da yi wa wannan matsala rikon sakainar kashi, lamarin da ya haifar da tsamin dangantaka a tsakanin hukumomin Mali da na Faransa.
Gugar zanar da firam ministan Burkina Faso ya fara yi wa kasashe aminai a game da wannan yaki makwanni kadan bayan juyin mulkin da ya dora Capitaine Ibrahim Traore a kan karagar mulki, alama ce da ke fayyace yunkurin kulla hulda da wasu manyan kasashen na daban irinsu Russia.
Saurari rahoton cikin sauti: