Ministan harkokin wajen Bénin ya gayyaci mukaddashiyar jakadan Nijar a Cotonou domin bayyana bacin ran gwamnatin kasarsa dangane da zargin da shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi na cewa mahukuntan Benin na da hannu a abin da ya kira yunkurin haddasa hargitsi a Nijar
Hukumomin mulkin sojan Nijer a karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tiani sun gana da sarakunan gargajiya domin sanar da su halin da kasar ke ciki a wannan lokaci na fama da kalubalen tsaro, da neman hadin kai a wurinsu
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Jamhuryar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya yi jawabi ga al’umma ranar bukin samun 'yancin kai inda ya tabo mahimman batutuwan da suka shafi tafiyar kasar daga lokacin da ya kwaci madafun iko zuwa yau.
Kasashen AES sun bada sanarwar yanke shawarar bai wa al'umomin kasashen ECOWAS ko CEDEAO izinin kai-komo a yankin AES Sahel ba tare da bukatar takardar bisa ba. Abin da ke zama wani matakin riga kafi, a dai dai lokacin da kasashen ECOWAS ke taro yau a Abuja kan batun ficewar su daga kungiyar.
A yayin da ECOWAS ke Shirin gudanar da taro a ranar lahadi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya domin tantauna makomar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso wadanda wa'adin ficewar su da ga kungiyar ke cika a watan janairun shekarar 2025, kasashen sun ce bakin alkalami ya riga ya bushe.
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a Nijar CODDH ta yi wa hukumomin mulkin sojan kasar hannunka mai sanda dangane da batun mutunta yarjeniyoyin kasa da kasa kamar yadda suka yi alkawari bayan juyin mulkin 26 ga watan Yulin bara, yayin da ake bikin ranar kare hakkin 'dan adam ta duniya ,
A yayinda ake bikin tunawa da ranar yaki da cin hanci ta duniya a yau 9 ga watan Disamba kungiyar Transparency International reshen Nijar ta bayyana damuwa game da abin da ta kira tarnakin da ake fuskanta a wannan gwagwarmaya sakamakon wasu dalilan da ke da nasaba da raunin doka
Yayin da al’ummar Ghana ke shirin halartar rumfunan zabe a ranar Asabar 7 ga watan Disambar 2024, ‘yan kasar mazauna Jamhuriyar Nijar sun bayyana manyan matsalolin da suke fatan sabuwar gwamnatin da za ta yi nasara a wannan fafatawa ta gaggauta magancewa
Wasu mutane sanye da kayan sarki a Nijar sun yi awon gaba da Moussa Tchangari jagoran kungiyar fafutuka ta Alternative, bayan da suka kutsa gidansa a daren jiya Talata jim kadan bayan dawowarsa daga Abuja kamar yadda wani na hannun damarsa Kaka Touda Goni ya bayyana wa manema labarai
Yayin da tawagar mataimakin Firai Ministan Rasha ta kammala rangadin kasashen Sahel da Nijar a karshen mako, wasu ‘yan kasar sun bayyana fatan ganin talaka ya amfana da wannan hulda, a daidai lokacin da ake fuskantar tabarbarewar dangantaka da kasashen yammacin duniya.
Kasar Chadi ta ba da sanarwar kawo karshen yarjejeniyar ayyukan sojan da ta sabunta da Faransa a shekarar 2019. Gwamnatin Chadin ta ce ta dauki wannan matakin ne da nufin jaddada ‘yancin kanta shekaru 66 bayan samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Jami’an hukumomin shige da fice ko Douane daga kasashen Afirka ta Yamma da ta Tsakiya sun fara gudanar da taro a birnin Yamai da nufin bitar halin da ake ciki a sha’anin shige da ficen kaya a kan iyakokinsu da neman hanyoyin magance wasu matsaloli.
A yayinda wa'adin cika shekara da ficewarsu daga kungiyar CEDEAO, ministocin cikin gidan Nijar, Mali da Burkina Faso sun amince da sabon samfarin fasfo da takardun kasa da za a fara amfani da su domin yin bulaguro a maimakon fasfon ECOWAS da ake amfani da shi a yanzu haka
EU ta janye jakadan na ta ne domin ta ji ta bakinsa bayan da gwamnatin Nijar ta zarge shi da saba ka'ida da saka son rai wajen kasafta wani tallafin jin kai na Euro milion 1.3 da kungiyar ta bayar domin agaza wa 'yan Nijar da ambaliyar ruwa ta shafa.
Shugabannin kungiyoyin kwadago da na jam’iyyun siyasa da jami’an fafutika masu yaki da akidar mulkin mallaka daga kasashen Afrika, Asia da na kudancin Amurka ne ke halartar wannan taro.
A wani abinda ke fayyace alamun baraka a tsakanin hukumomin Mali, fira ministan gwamnatin rikon kwaryar kasar, Dr Choguel Maiga ya caccaki shugaban rikon kwaryar kasar, Janar Assimi Goita da mukarrabansa.
Malaman makaranta a Jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwana biyu daga yau Litinin da nufin tada hukumomi daga barci a game da wasu dadaddun bukatun da suka ce an yi biris da su duk kuwa da cewa magana ce ta kyautata rayuwar malamai
Kungiyar Transparency International ta gargadi mahukuntan Jamhuriyar Nijar da su soke yarjejeniyar ayyukan gina matatar da suka cimma da kamfanin Zimar na kasar Canada bayan da ta ce bincikenta ya gano cewa kamfanin Zimar na daga cikin irin kamfanonin da ke kewaye wa hanyoyin biyan haraji
Domin Kari