Kungiyar tarayyar turai ta ayyana shirin bada tallafin makamai wa wasu kasashen Afrika masu fama da matsalolin ta’addanci wadanda suka hada da Jamhuriyar Nijer da Somalia
Kungiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa Reporters Sans Frontieres wato RSF a takaice ta bayyana damuwa a game da abinda ta kira yanayin tsaka mai wuyar da ‘yan jarida suka shiga a yankin Sahel.
An fara samun nasarar ayyukan tsaro na hadin gwiwa tsakanin kasashen Mali da Nijar masu fama da matsalar rashin tsaro.
Wannan yunkuri dai wani bangare ne na fafutukar ganin mutanen da ke tawaya sun mori ‘yancin da ke kunshe cikin yarjeniyoyin da kasashe suka cimma da Majalisar Dinkin Duniya.
Jami’an hukumar kula da shige da fice Kwastam na jamhuriyar Nijar sun fara yajin aikin kwanaki biyu da nufin nuna rashin nuna rashin jin dadinsu game da tsarin daukar sabbin ma’aikata na gwamnatin kasar.
Wasu ‘yan ci rani ‘yan asalin kasashen yammacin Afrika da aka tuso keyarsu daga Libya, sun yi zaman dirshan a ranar Litinin a ofishin hukumar kula da kaurar al’umma IOM, dake birnin Yamai da nufin nuna kosawa da rashin mayar da su gida kamar yadda aka yi masu alkawali a baya.
Sakataren harakokin wajen Amurka Antony Blinken da ke ziyarar wuni biyu a jamhuriyar Nijar ya sanar da karin kudaden tallafi ga kasashen yammaci da tsakiyar Afrika wadanda za'a yi amfani da su don inganta rayuwar al’umomin wadannan kasashe.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya isa Jamhuriyar Nijar a yau Alhamis 16 ga watan Maris inda zai tattauna da takwaransa Hassoumi Massaoudou ( Hasumi Masa’udu) kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu masu dadaddiyar huldar diflomasiya.
Shugaban kasar Nijer ya fara rangadi a jamhuriyar Benin, don tantauna da takwaransa kan batutuwa da dama da suka shafi huldar kasashen biyu, a daidai lokacin da ayyukan ta’addanci daga arewacin Mali ke shafar kasashen biyu.
Masana harkokin tsaro sun bayyana gamsuwa da abin da suka bayyana a matsayin kusancin da aka fara samu a tsakanin hukumomin Nijar da na Mali, wadanda a baya ba sa ga maciji sakamakon juyin mulkin da soja suka yi a kasar ta Mali.
Hukumar kula da samar da abinci ta MDD ta tallafa wa ‘yan gudun hijirar cikin gida a jihar Tilabery ta Jamhuriyar Nijar da kudade da nufin sassauta wahalwalun da suka shiga na tserewa daga matsugunansu na asali sanadiyar aika-aikar ‘yan ta’addan arewacin Mali.
A yayinda a yau Laraba 8 ga watan Maris ake bukukuwan ranar mata ta duniya mata a kauyen Kouraye dake jihar Zinder a jamhuriyar Nijer sun dukufa ka’in da na’in a karkashin wani shirin da hukumar WFP da FAO da asusun IFAD suka kaddamar.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron da ke rangadi a wasu kasashen yankin tsakiyar Afrika ya yi ikirarin cewa zamanin siyasar uwar daki da ‘yan korenta a tsakanin Faransa da kasashen Afrika ya wuce.
Galibin ‘yan Najeriya mazauna Nijar da suka bayyana ra’ayoyi a kan zaben kasar na 25 ga watan Fabrairu da ya gabata, na cewa sun yi na’am da sakamakon da INEC ta ayyana.
Shugaban kasar Nijar Mohmed Bazoum ya aika da sakon taya murna ga ‘dan takarar jam’iyar APC Bola Ahmed Tinubu wanda hukumar INEC ta ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Najeriya da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrerun 2023.
Wasu kungiyoyin yaki da tsatsauran ra’ayi a Najeriya da Nijar sun kaddamar da wani shirin yawarwa da nufin fadakar da matasan kasashen yankin Sahel game da hanyoyin kare kai daga fadawa tarkon ‘yan ta’adda.
Domin Kari