Kungiyar ta EU ta kuduri aniyar bada tallafin ne a yayin da kasashen suke ci gaba da neman hanyoyin murkushe tashin hankalin da suke fuskanta shekaru da dama kamar yadda suka dade suna nema.
Sai dai masana na bayyana ra’ayoyi mabambanta dangane da fa’idar wannan yunkuri na kungiyar EU.
Shugaban sashen kula da siyasar tarayyar turai na kasashen waje Joseph Borell da yake jawabi a yayin taron tsaron da ya gudana a makon jiya a Brusells ya tabbatar da wannan aniya ta bayar da tallafin makamai samfarin Armes Letales wa kasashen Nijer da Somalia, ya na mai cewa," sanannen abu ne abokan huldarmu na kara nuna bukatar samun tallafin bindigogi kwarai irin abinda muka yi wa Ukraine muna iya yin sa kuma za mu yi shi domin wasu."Matakin da masani akan sha’anin tsaro Amadou bounty Diallo ya yaba domin a ra’ayinsa alama ce dake nunin cewa kasashen yammacin sun gamsu da jajircewar Nijer a yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Kyakyawar huldar dake tsakanin Kungiyar Tarayyar Turai da gwamnatocin Nijer da ta Somalia da kuma yadda wadanan kasashe suka ki sakarwa a kamfanin sojan haya na Wagner Ballantana fuska ya sami sukunin kulla wata mu’amula na daga cikin hujjojin da aka dogara da su wajen amincewa bada wannan tallafi.
Kawo yanzu, ba a bayyana ranar da za a bada wannan tallafi na makaman Kungiyar EU ba, ballantana batun sanin adadinsu a yayinda yaki da ta’addanci ke kara zafi a yankin Sahel.