Kungiyar ma’aikatan kamfanonin wayar sadarwa a Jamhuriyar Nijar ta bayyana matsayinta bayan da hukumomi suka ci tarar kamfanonin wayar sadarwa sakamakon zarginsu da saba yarjejeniyar aiki .
Wani ‘dan sanda a Jamhuriyar Nijar ya hadu da ajalinsa a yammacin jiya bayan da jami’an tsaron Jandarma suka bude masa wuta lokacin da ya shiga jami’ar Yamai da daddare dauke da makami cikin wani yanayi mai duhu.
A taron manema labaran da suka kira a ranar litinin 17 ga watan Yuli, shugabanin hukumar ARCEP sun fara ne da yin bayani game da binciken da jami’an hukumar suka gudanar a yankunan da jama’a suka koka da rashin ingancin layin wayar salula a shekarar 2021.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun ba da sanarwar rufe wasu makarantu masu zaman kansu da suka hada da na Firamare da sakandare a jihohin Dosso Yamai Maradi da Zinder, sakamakon zargin keta ka’ida.
A yayin da batun ‘yan luwadi da ‘yan madigo da ta masu auren jinsi ke ci gaba da haddasa mahawara a kasashe daban-daban hukumomin Jamhuriyar Nijar sun jaddada aniyar kafa dokokin hukunta wadanda aka kama da aikata irin wadanan dabi’u a kasar.
Yau aka fara gudanar da taron Amurka da kasashen Afrika a birnin Gaborone na kasar Botswana karo na 15 wato US Africa Business Summit.
Masu ruwa da tsaki a sha’anin sufuri a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da wani taro domin tunatarwa akan dokar da ta kayyade lodin da ya zama wajibi ga motocin dakon kaya shekaru sama da 15 bayan da kasashen yammacin Afrika membobin kungiyar UEMOA masu amfani da kudaden cfa suka bullo da shi.
A yayinda wasu kasashe irinsu Najeriya suka yi nisa a ayyukan mayar da Alhazzai zuwa gida bayan kammala aikin Hajji, kamfanonin da aka ba kwangilar jigilar Alhazzan Jamhuriyar Nijar sun bayyana kokarin da su ke yi na mayar da mahajjatan kasar gida.
Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijer ta bayyana samun nasarar kama wasu gaggan ‘yan ta’adda da kasar Burkina Faso ta dade ta na nema ruwa a jallo, sakamakon ta’asar da suke jagoranta a yankin iyakar kasashe 3 a makon da ya gabata.
A jamhuriyar Nijer mako 1 bayan bayyanar sakamakon jarabawar daliban da ke neman takardar shaidar kammala karatun share fagen shiga jami’a, gwamnatin kasar ta yanke shawarar bai wa wani rukunin dalibai damar sake rubuta gwajin lissafi sakamakon wasu kura-kuran da aka gano a gwajin.
Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya jagoranci bikin kaddamar da wata tashar samar da wutar lantarki da hasken rana a birnin Yamai a ci gaba da neman hanyoyin warware dadadiyar matsalar wutar da ake fama da ita a kasar da ke sayen wani bangaren wutar lantarki daga kamfanonin Najeriya.
Masu sharhi akan sha’anin tsaro sun hango cewa kungiyoyin ta’addancin Arewacin Mali sun fara yunkurin kafa reshe a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda bayanai ke nunin yadda suke sajewa da jama’a su na ratsa wasu jihohin Jamhuriyar Nijar don shiga Najeriya cikin ruwan sanyi.
‘Yan kasar Senegal mazauna jamhuriyar Nijer sun bayyana farin ciki bayan da shugaba Macky Sall ya sanar cewa ba zai yi tazarce ba a zaben da za a yi a watan fabrerun 2024 koda yake a cewarsu lamarin na bukatar taka-tsan-tsan.
Matsalar wutar lantarki a jamhuriyar Nijer ta haifar da damuwa a wajen al’umma sakamakon lura da yadda a ‘yan kwanakin nan a ke fuskantar daukewar wuta akai-akai inda a kowace rana akan shafe lokaci mai tsawo ba tare da an sami wutar ba lamarin da ke shafar al’amuran rayuwar yau da kullum.
A shirin Nakasa na wannan makon har yanzu muna tare ne da wani dan asalin jihar Adamawa da ke zaune a jihar Enugu a yankin Kudu maso gabashin Najeriya, wanda ya tsinci kansa cikin wannan hali bayan da ya yi fama da rashin lafiya a lokacin da yake karami.
A yayin da yake bitar karshen aiyukan jigilar maniyata zuwa kasa mai tsarki a albarkacin hajin shekarar 1444 da ke dai dai da shekarar mai ladiya ta 2023 shugaban hukumar alhazzan Nijer Commissaire Ibrahim Kaigama, ya tabbatar da cewa an yi nasarar isar da dukkan maniyatan kasar a kan lokaci.
A jamhuriyar Nijer samfarin sabon taken kasar da majalissar dokoki ta yi na’am da shi a zamanta na ranar alhamis ya haifar da dambarwa a tsakanin al’ummar kasar.
Majalissar dokokin Jamhuriyar Nijer ta yi wa ayar farko ta kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska da nufin samun sukunin shigar da sabon taken kasar da zai maye gurbin wanda ake amfani da shi tun a jajibirin samun ‘yancin kan kasar daga turawan mulkin mallaka.
Domin Kari