Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fafutuka Sun Bukaci A Yi Sulhu A Rikicin Siyasar Nijar


Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO
Zauren taron kungiyar ECOWAS/CEDEAO

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama sun bukaci bangarorin da ke takaddama a rikicin siyasar da ya sarke a kasar da su rungumi hanyar sulhuntawa da juna.

Wannan na zuwa ne bayan da sojoji suka kifar da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum daga karagar mulki, lamarin da kungiyar kasashen ECOWAS ta ce ba za ta sabu ba.

ECOWAS ta kuma yi barazanr amfani da karfin soja mudddin masu juyin mulkin ba su mayar da ragamar mulki a hannun hambararen shugaban ba.

Kungiyar ta CEDEAO ta kakaba wa kasar ta Nijar takunkumi da nufin tilastawa sojoji bin umurninta.

Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer
Sojojin CNSP da suka yi juyin mulki a Nijer

Sai dai a wata hira da wakilinmu Souley Moumouni Barma, Alhaji Salissou Amadou na kungiyar RNDD ya bukaci a dubi halin da talakawa za su shiga sakamakon wannan kiki-kaka.

Saurari cikakken hirarsu a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG