‘Yan bindigar ‘dauke da makamai sun afkawa masu gadin na’urorin dake samar da wutar lantarki akan titin Murtala Mohammad, da missalin karfe biyu da rabe na dare a ‘karshen mako. Inda suka yi awon gaba da babbar wayar dake samar da hasken wutar lantarki mai suna XLP Cable, al’amarin da ya jefa yankin mahadar Banex zuwa Gwarinpa a cikin duhu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin kakakin Ministan Abuja, Alhaji Abubakar Sani, yace bayan sace wayoyin dake samar da wutar lantarki ‘yan bindigar sun raunata masu gadin gurin. ya kara da cewa sakamakon faruwar lamarin wasu tituna masu yawa na zaune ba tare da wutar lantarki ba, hakan kuwa bai yiwa hukumar birnin tarayya dadi ba.
Karuwar aikace-aikacen miyagun mutane ‘dauke da bindigogi a Abuja ba wani bakon abu bane, kama daga wadanda ke kwace motocin jama’a da bakin bindiga zuwa ga miyagun barayi na musamman da ake kira ‘yan One Chance, da kuma wadanda ke shiga gidajen mutane su kulle masu gidan su tafka aika-aika a kowanne lokaci.
Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina daga babban birnin tarayya Abuja.
Facebook Forum