Rikicin Boko Haram dai ya jefa dubban mutane cikin halin iftila’i, hakan yasa aka fara wannan shiri da mata 150 a garin Maiduguri, da kuma ake sa ran za a baiwa mata dubu goma-goma horo a kowacce jiha, kan sana’o’i daban-daban don su kasance masu dogaro da kai.
Yanzu haka dai ana kiyasin mata fiye da dubu 30 ne suka rasa mazajensu sakamakon rigingimun ‘ya ‘yan Boko Haram, wadanda mafi yawansu ke rike da marayu wadansu ma basu san inda ‘ya ‘yan nasu suke ba.
Kwamishinar ma’aikatar harkokin mata ta jihar Borno, Fanta Baba Shehu, ta tabbatar da cewa a kowacce jiha mata dubu goma zasu amfana da wannan shiri da aka kaddamar inda aka fara da mata 150. Shiri na biyu kuma da za a yi zai hada mata da maza wadanda suka rasa mazajensu ko mutsugunnan su.
Shugabar kungiyar gamayyar kungiyoyin mata ta jihar Borno, Hajiya Yaya Gana Alkali, ta yaba da wannan shiri na tallafawa kasancewar yanzu haka akwai mata sama da dubu biyar dake bukatar taimako.
Shirin dai zai baiwa matan da suka rasa mazajensu ko kuma suke fama da kuncin rayuwa wajen koyon sana’o’i daban-daban a fadin jihar, wanda ya hada da koyon yin Sabulu da koyon Rini da kuma lemukan sha.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum