Dan takarar shugabancin Faransa Francois Fillon, mai ra'ayin rikau, wanda tuni yake fama da wasu matsaloli, yayi nemi gafara saboda kalaman batunci ga yahudawa da ake zargin jam'iyyarsa tayi kan wani abokin karawarsa Emmanuel Macron.
A Haiti, akalla mutane 34 ne suka halaka, bayanda wata motar kiya-kiya wacce ta kade mutane take neman gudu ta fada cikin taron mutane jiya lahadi a birnin da ake kira Gonaives, kamar yadda jami'an kasar suka yi bayani.
‘Yan gudun hijira sama da 3000 sun koma muhallansu a karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa, sakamakon nasarar da rundunar soja ke samu na dakile hare-haren kunar bakin wake da na sari ka noke.
Rundunar sojan Najeriya na ci gaba da bude sabbin rundunoni da bataliyoyi a sassa daban-daban na kasar.
Cibiyar tallafawa masu larurar yoyon fitsari dake a Asibitin Jankwano a Jos, ta ce ta gudanar da aikin tiyata ga mata fiye da Dubu 10, kuma dukkansu suna cikin koshin lafiya.
Hatsarin mota yayi sandiyar rayukan mutane sama da 30 tare da raunata wasu da yawa, kan hanyar zuwa Ngurore dake jihar Adamawa.
Rashin abin yi ga matasan Afirka zai ci gaba da zamewa babban barazana ko da kuwa sojoji sun yi nasarar kakkabe yan ta'adar dake nahiyar, in ji Janar Thomas Waldhauser babbab hafsan sojan Amurka dake kula da ayyukan soja a nahiyar Afrika.
Tawagar Masu bincike ta fannin kimiyya sunyi anfani da shebur domin kwashe kasar da aka rufe kabarin da aka binne mutane da yawa a garin Barbera dake Somaliland.
A wani mataki na rage cunkoso a gidajen yari, an sallami wasu fursunoni 92 daga gidajen yari biyu dake Minna a jihar Neja.
Wata kotun Amurka a Minnestoa, jiya Laraba, ta daure wani mutum mai suna George Fisher shekara daya a gidan yari, saboda ya yi barazanar zai kai wa wani masallaci dake birnin hari.
Rundunar sojan Najeriya ta kaddamar da kwamitin da zai binciki zarge-zargen take hakkin bil Adama da wasu kungiyoyin rajin kare hakkin ‘dan Adam ke yi wa sojoji.
Babbar hukumar leken asiri ta Amurka CIA, ta fito fili tana bayyana damuwarta kan fallasar da dandalin tsegumi WiKiLeaks yayi, hukumar tana gargadin cewa "tilas Amurkawa duka su damu kan makomar wannan mataki.
A kudancin Sudan ta kudu mazauna kauyuka sun ce sojojin kasar da ake kira SPLA sun yi barna a yankin da ake kira Oming, bayan da wasu 'yan bindiga suka kai hari wanda ya halaka dakarun kasar takwas, ya jikkata wasu biyar a farkon makon nan.
An yi wa wasu yara biyar almajirai dake karatun Islamiya na allo yankan rago a jihar Neja.
Ranar takwas ga watan Maris rana ce ta mata a duniya kuma rana ce da aka ware domin yin dubi kan irin dumbin matsalolin dake addabar mata a duk fadin duniya.
Yanzu haka ‘yan Najeriya matafiya a ciki da waje, sun kuduri aniyar fuskantar matsalolin da ba a rasa ba domin kulle tashar jirgin sama ta babban birnin Abuja.
Babban Bankin Najeriya yace zai ci gaba da samar da daloli cikin kasuwar hada hadar kudade har sai darajar Naira ta dawo.
Tsohon gwamnan jihar Adamawa da kotu ta daure na tsawon shekaru biyar a gidan kaso, Bala James Ngillari, tare da kwamishinoninsa da magoya bayansa sun ce zasu daukaka kara game da hukuncin.
Majalisar Wakilan Najeriya za ta tura wani kwamiti na musamman zuwa kasar Afirka Ta Kudu, don bin kadun `yan kasar da aka kai wa harin kyamar baki.
Domin Kari