Domin tuna wannan rana Muryar Amurka ta shirya wani wata tattaunawa da ta karbi bakuncin wasu mata daga wasu kasashe biyu a cikin kasashen dake fama da ‘yan ta’adda, wato Najeriya da Somalia inda suka ba da labarinsun kan halin da su ke ciki.
Darektar Muryar Amurka Amanda Bennett ce ta jagornci wannan tattaunawa wacce aka dauka ranar Litinin da ta gabata.
Najeriya dai ta jima ta na fama da ayyukan ta’addancin Boko Haram kuma a wata mai zuwa ne za a cika sheakru uku da yin garkuwa da yaran matan makarantar Chibok su 276 wanda galibinsu har ya zuwa yau ba a san inda suke ba.
A lokacin wannan tattaunawa, daya cikin iyayen wadannan yaran mata wato Rebecca wacce aka sace ‘yar ta Sarah Samuel, ta ce ta yi kwanaki dubu daya da 59 ba ta ganta ba, kuma ta fashe da kuka a lokacin da ta yi kokarin yin tsokaci a lokacin tattaunawar da aka yi da ita ta kafar tauraron dan adam a ranar Litinin.
A gabashin Afrika kuwa, Somaliya tana kokarin ficewa daga yakin basasan da aka kwashe shekaru 20 ana yi, da kuma barazanar ‘yan ta’addan al-Shabab, kazalika yankin na fama da tsananin fari domin ko a makon da ya gabata mutane 110 ne suka mutu tsakanin sa’oi 48 saboda matsalar mummunan farin da ba a taba gani ba a kasar.
Facebook Forum