Noma Tushen Arziki
Ma'aikatar Tsaron Amurka ta bayyana harba makamani mai linzamin da Koriya Ta Arewa ta cilla na bayan-bayan nan, a matsayin "wata babbar barazana" sannan ta ce ta na daukar mataki game da makami mai linzami na wannan kasa mai ra'ayin gurguzu.
Wani babban kwamandan sojin Sudan Ta Kudu, wanda ya balle a watan jiya, ya ce shi ma yanzu ya kafa tasa kungiyar 'yan tawayen don yakar Shugaba Salva Kiir.
Jiya Litini Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wani sabon umurninsa na matsayin Shugaban kasa, na hana shigowa Amurka daga wasu kasashe 6 na tsawon watanni uku, da kuma hana duk wani dan gudun hijira shigowa na tsawon watanni hudu, bayan da alkalan kotun daukaka kara ta tarayya su ka hana wani umurni makamancin wannan aiki a watan jiya.
Gwamantin Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da su dakatar da bulaguron da suke shirin yi zuwa Amurka, har sai an fahimci inda manufofin shugaba Donald Trump kan baki ya sa gaba.
Manyan dattawan jam’iyyar adawar Najeriya PDP da sauran masu ruwa da tsaki zasu gana da shugaban jam’iyyar Sanata Ali Modu Sheriff, don dinke barakar jam’iyyar da kaucewa jiran hukuncin da ba a san ko me zai fito ba daga kotun koli.
Biyo bayan hukuncin da wata babbar kotu a jihar Adamawa ta yanke wa tsohon gwamnan jihar James Bala Ingilari, daurin shekaru biyar a gidan kaso saboda sabawa ka'idojin bayar da kwangila, yanzu haka al’umman jihar da kuma masana sharia na tsokaci.
Da safiyar yau Litinin Koriya Ta Arewa ta harba makamai masu linzami guda hudu, uku daga cikinsu sun yi tafiyar kilomita dubu daya kamin su fada cikin teku, kilomita 350 kacal daga Japan, kamar yadda jami'an Koriya Ta Kudu da Japan suka yi bayani.
A yau Litinin ake sa ran shugaban na Amurka zai sanya hannu kan sabuwar doka da zata haramtawa wasu rukunin mutane shigowa Amurka, wannan matakin ya biyo bayan da wata kotun daukaka kara ta dakatar da aiki da mfani da dokar ta farko.
Wani hafsa a rundunar sojojin Najeriya yace harin da aka kai bisa kuskure akan sansanin 'yan gudun hijira a yankin arewa maso gabashin kasar, ya auku ne saboda bayanai da ba dai-dai ba.
A karo na biyu fadar shugaban Najeriya ta ce bata jin dadin yadda wasu ‘yan tsiraru ke son shiga tsakanin shugaba Mohammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Osinbajo, bisa ci gaban da ake samu a kasar.
Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya MDD sun ziyarci jihar Borno, don ganin yadda lamarin tsaro yake da kuma halin da al’ummar da rikicin Boko Haram ya rutsa ke ciki.
Al’ummar Fulani mabiya addinin Krista sun gudanar da addu’o’i na musamman domin samun zaman lafiya a Najeriya da sauran sassan Duniya.
Dubban jama’a ne Musulmi da Kristoci suka fito kwansu da kwarkwata a garin Jalingo, dake zama fadar jihar Taraba, domin gabatar da addu'o'i na musamman don rokon Allah ya bai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, lafiya.
Babban atoni janar na Amurka Jeff Session, yace ya tsame kansa daga duk wani binciken zargin da ake yiwa Rasha na yin kutse a zaben Amurka wanda akayi a shekarar data gabata.
Shugaban Amurka Donald Trump yayi alkawarin bunkasa fannin tsaro na Amurka.
A jihar Florida ta leko ta koma, ga matar mutumin nan da ya kashe mutane har 49 a wani gidan rawa. Domin kuwa alkali ya sake ta amma kuma wani alkali ya sake kama ta.
Ma’aikatan gwamnatin jihar Kogi dake tarayyar Najeriya sun kwashe watanni 12 ba tare da an biya su albashinsu ba.
Hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya ta wanke sojojin kasar daga zargin da kungiyar Amnesty Internatioanl ta yi na cewa sojojin Najeriya na take hakkin bil Adama.
Duk da cewa Alkalai a Amurka sun takawa dokar farko birki, yanzu haka gwamnatin Trump na ci gaa da yiwa dokar kwaskwarima don sake gabatar da ita.
Domin Kari