Wannan al’amari dai ya faru ne a garin Tungar Magajiya, da ke yankin karamar hukumar Rijau. Maharan da suka aikata wannan ‘danyen aikin da ba a san ko su waye ba, sun afkawa almajiran ne a lokacin da suke barci suka yan-yanka musu wuya da wani abu da ake kyautata tsammanin yayi kama da mashi.
Mallam Muhammadu Bala, wanda yake ‘daya daga cikin malaman almajiran, ya ce cikin dare ya farka ya ji yaran sun farka suna kuka inda ‘daya daga cikinsu yace “Wayyo an kashe wane”. Kuma ya tabbatar da cewa lamarin ya faru a makarantu biyu, wanda a makarantarsa aka yanka yara biyu, sauran ukun kuwa a wata makaranta ta daban abin ya faru.
Shugaban karamar hukumar Rijau, Bello Bako, ya ce wannan shine karo na farko da aka taba samun faruwar irin wannan abu, kuma yanzu haka suna cikin bakin ciki. Haka kuma ana gudanar da addu’o’in Allah ya tona asirin wadanda suka aikata wannan barna.
Ita rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar da afkuwar wannan al’amarin, kakakin ‘yan sandan jihar DSP Bala El-kana, yace duk da yake kawo yanzu basu sami nasarar kama kowa ba, amma suna kan gudanar da bincike.
A halin da ake ciki kuma rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ta samu nasarar kama wasu mutane 20 da ake zarginsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa wani jami’in ‘yan sanda mai mukamin DCO a Minna, a karshen makon da ya gabata.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.
Facebook Forum