A yau Asabar shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya sauka a birnin Abuja, bayan Kwashe sama da watanni uku yana jinya a birnin London dake Burtaniya.
Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na dab da yanke hukunci kan hanya mafi kyau da zata bi wajen tunkarar yakin kasar Afghanistan da ya kwashe shekaru 16 ana yi.
Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a dalilin zaizayar kasa a Saliyo na ci gaba da karuwa, yayin da yawan ruwan sama ke kawo cikas ga aikin ceton wadanda suka bata.
Fara Ministan Spain ya ayyana kwanaki uku domin zaman makoki da jimamin mutanen da suka rasa rayukansu a harin da aka kai da mota ranar Alhamis.
Noma Tushen Arziki
Ambaliya ruwa sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi sanadin rayukan mutane sama da 30 a kasar Nepal.
Wani jagora a kungiyar 'yan ta'addar Al-shabab ya mika wuya ga gwamnatin kasar Somalia.
Biyo bayan baiwa hammata iska da aka yi a taron gangamin turawa jar fata masu fifita jinsin turawa da kuma ‘yan zanga zangar da suka fito yin adawa da wannan gangamin a Jihar Virginia, an fara gudanar da bincike kan wani mai mota da ya kashe wata mata.
Kafofin yada labaran gwamnati a Hadaddiyar Daular Larabawa sun ce sojojin daular su 4 sun mutu a lokacin da wani jirgin sama mkai saukar ungulu ya fadi a kasar Yemen.
Kimanin mutane tara ne suka rasa rayukansu a wani tashin hankali da ya barke bayan da aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasar Kenya.
An yi arangama tsakanin wasu turawa masu gangamin fifita jinsinsu da wasu masu adawa da wannan gangamin a jihar Virginia.
Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Najeriya ta ce jami’anta sun damke wasu manyan kwamandojin Boko Haram a jihohin Kano da Kaduna da Taraba.
Yau ranar Asabar 12 ga watan Agusta ranace da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin bikin ranar matasan duniya.
Shugaba Paul Kagame shine kan gaba da kuri’u a zaben shugaban kasar da aka gudanar, a cewar Hukumar zaben kasar.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya mayar da martani game da takunkumin da Amurka ta kakaba masa.
Shugaban Amurka Donald Trump ya kara tsananta furucinsa kan kasar Koriya ta Arewa game da barazanar da ta yiwa Amurka.
Rundunar Sojan Amurka ta dakatar da aikin nemo sojojin kundunbala uku da suka bace bayan da jirginsu yayi hatsari cikin teku.
Domin Kari