A jiya Alhamis ne shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ce, yana son ya gana da mutumin da ya kakaba masa takunkumi, wato shugaban kasar Amurka Donald Trump, yana mai Allah wa dai da abin da ya kira rashin adalci.
Cikin wani jawabi da ya gabatarwa sabbin ‘yan Majalisun yiwa Kundin Tsarin Mulkin kasar kwaskwasrima da aka zaba su 545, Maduro ya ce, ya umarci ministan harkokin wajen kasar da ya tuntunbi Amurka domin su saka ranar ganawa ko tattaunawa ta wayar talho tsakaninshi da Donald Trump.
Shugaban na Venezuela ya kuma ce ya bayar da umarni, idan da hali, yana son ganawa da Trump a gefen babban taron shekara-shekara na shugabannin kasashen duniya na MDD da za a gudanar ranar 20 ga watan Satumbar wannan shekara.
Bayanan Maduro na zuwa ne lokaci kalilan bayan da Venezuela ta gargadi shugaban na Amurka da cewa Venezuela ba zata taba bada kai bori ya hau ba, a cece-kuccen da ake tsakanin kasashen biyu.
Gwamnatin Trump dai ta kira gwamnatin Maduro a matsayin gwamnatin kama karya, ta kuma kakaba masa da jami’ansa masu yawa takunkumi ranar 31 ga watan Yulin da ya gabata.
Facebook Forum